Ƙungiyar nan ta likitocin kula da lafiya kyauta ta ‘Medicins Sans Frontieres, MSF ta bayyana cewa idan fa bala’in hare-haren ‘yan bindiga ya ci gaba da muni a yankin Arewa maso Yamma, to jama’ar yankin za su ƙara fuskantar matsalar kasa samun kula da lafiya.
Wannan ƙungiyar jinƙai ta bayyana cewa saboda a 2023 fiye da ƙananan yara 854 ne suka mutu a cibiyoyin ta daban-daban na jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina, sanadiyyar hare-haren da suka haddasa wa yaran rashin abinci mai gina jiki da ƙarancin samun kula da lafiya.
MSF ta ce jami’an kula da lafiyar su a jihohi biyar daga cikin jihohin Arewa maso Yamma, sun bayar da magunguna tare da kula da lafiyar yara 171,465 marasa abinci mai gina jiki a cikin shekarar 2023.
MSF ta ce ta kai wasu mutum 32,104 an kwantar da su asibiti, sanadiyyar ciwon da ke neman halaka su saboda rashin abinci mai gina jiki.
Ƙungiyar ta ce an samu ƙarin yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki a 2023 da kashi 14 bisa 100 idan aka kwatanta da 2022.
“Al’ummar da ke zaune a yankunan karkarar jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina da Kebbi su na fama da munanan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai masu ba ƙaƙƙautawa. Cikin shekarar da ta gabata, an kashe sama da mutum 2,00 a hare-hare fiye da 1,000 a yankin, kamar yadda ƙididdigar ACLE ta nuna.
“Haka kuma mutane na rasa muhallin su, su na tserewa gudun hijira, dama sun rasa abincin su da kayayyakin da suka dogara da su. Kuma sun daina zuwa gonakin su domin su yi noma. A kullum sai sun fita neman abincin da za su ci su da iyalan su. Kuma samun damar kula da lafiyar su abu ne mai hatsarin gaske.” Inji MSF.
Discussion about this post