Kamfanin raba wutar lantarki DisCo dake Jos a jihar Filato sun yi kira ga kwastamominsu dake jihar Gombe da su bada kuɗi don gyaran tiransifoma idan ya lalace koda ko ma’aukata ne syka nemi su bada kuɗi kafin a gyara.
Babban jami’in tsaro na Kamfanin Musa Abdullahi ya sanar da haka a Gombe ranar Litinin inda yake cewa ba hakkkin su bane su gyara tiransifoma ba.
Abdullahi ya kara da cewa hakin mutane ne su sanar da Kamfanin DisCo mafi kusa da su idan taransfoma ya lalace sannan kada su ba ma’aikata kudi don gyara.
Ya ce akwai lokuta da dama da aka sa mutane su hada kudade domin gyaran taransfoma ko siyan sabo inda yake cewa hakan ba daidai ne ba domin hanya ce da ake amfani da shi don zambatar mutane.
Ya yi kira ga mutane da su riƙa gaggawar kai karan duk wani ma’aikaci da ya nemi a biya kuɗi don gyaran tiransifoma a lokacin da za a gyara shi.
“Idan har taransfoma na Unguwar da kuke ya lalace kamata ya yi a sanar da Kamfanin DisCos sannan idan har ba za a iya jira har Kamfanin ta zo ta gyara ba za a iya rubuta wa manajan Kamfanin da manajan shiya na Kamfanin wasika domin bada gudunmawar su don gyara taransfoman.
A ƙarshe Abdullahi ya yi kira ga mutane da su rika yi wa ma’aikata adalci a lokacin da suke aikin su.
Discussion about this post