Gwamnatin Kaduna ta ƙaryata labarin da jaridar Punch ta buga ranar Asabar cewa wai gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Uba Sani ta ɗauko hayar mai shiga tsakani domin a karɓo ɗaliban kuriga daga hannun ƴan bindiga.
A wata sanarwa ta musamman ranar Asabar, kakakin gwamna Sani, Mohammed Shehu ya ce gwamnatin Kaduna ta nisanta kanta daga wannan zargi.
” Rahoton cewa wai gwamnatin Kaduna ta ɗauko hayar mai shiga tsakani domin kuɓutar da yara da malaman makarantar kuriga, ƙarya ce, babu wannan magana. Jaridar Punch bata faɗi gaskiya ba.
” Abinda muke so mu faɗi a nan shine gwamnatin mu bata ra’ayin tattaunawa da ƴanta’adda, kuma ba za mu yi haka ba saboda ko a baya muna adawa da hakan.
Jaridar PUNCH ta buga cewa majiya daga cikin fadar gwamnatin Kaduna ta shaida mata cewa tuni gwamnatin Uba Sani ta kinkimo mai shiga tsakani domin a dawo da ɗaliban da aka sace tare da malamansu a Kuriga, dake ƙaramar hukumar Chikun.
Punch ta ce majiyar wanda suka nemi a ɓoye sunayen su sun shaida wa jaridar cewa mai shiga tsakanin ya kware matuka wajen tattaunawa da ƴanbindiga don ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Dama kuma idan ba a manta ba, gwamna Sani ya yi wa iyaye da ƴanUwan waɗanda aka sace alƙawarin za adawo da duk wanda aka sace cikin koshin lafiya.
Ya ce gwamnati za ta yi kokarin ganin ta ceto yaran ba tare da an samu wata matsala ba.
” Na sanar da shugaban kasa da kuma Nuhu Ribaɗu, kuma duk sun ce gwamnati za ta tabbatar da an ceto waɗanda aka sace cikin koshin lafiya.
Discussion about this post