Rahotanni sun tabbatar da cewa aƙalla ɗalibai ‘yan firamare da na sakandare 287 ne ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a ƙauyen Kuriga, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, a safiyar Alhamis.
Gidan Radiyon BBC ya ruwaito cewa wani malamin makaranta mai suna Sani Abdullahi, ya bayyana yadda ya kuɓuta, kuma ya tabbatar da cewa ɗalibai 287 ne aka sace a safiyar.
“A ɓangaren sakandare ɗalibai 187 suka ɓace, a ɓangaren firamare kuma ɗalibai 125 ne da farko ba a gani ba. Amma daga bisani guda 25 sun dawo.”
Malamin ya bayyana haka a lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya ziyarci makarantar, domin gani da ido kan yadda lamarin ya ke.
Ya ce, “na shigo makaranta misalin ƙarfe 7:45 na safe, sai na shiga ofishin shugaban makaranta ɓangaren sakandare. Kawai sai ya ce min in waiga baya. Ina juyawa sai na ga ‘yan bindiga sun kewaye makarantar.
“Mun ruɗe ba mu san inda za mu ba. Kafin su shiga da mu daji sai muka canja hanya,” inji Sani Abdullahi.
Ya ce mahara sun kashe mutum ɗaya, sauran yaran da aka gudu da su ɗin shekarun su sun kama ne daga 28 zuwa 15.
Wani kuma ya ce babu gidan da wannan lamari bai shafa ba a Kuriga.
Kalaman Ministan Tsaro Ƙasa Da Sa’o’i 48 Kafin A Sace Ɗaliban:
Jim kaɗan bayan ɓullar mummunan labarin sace ɗaliban Kuriga 287, a garin wanda ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, mutane da dama sun waiwaya sun tuna kalaman da Ministan Tsaro, Muhammad Badaru ya yi a Kaduna, ƙasa da sa’o’i 48 kafin sace yaran.
Badaru ya bayyana cewa dalilin ci gaba da kai hare-haren da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke yi a yankunan Arewa, shi ne saboda rashin wadatattun sojoji.
Ministan Harkokin Tsaro, Muhammad Badaru, ya bayyana cewa matsalar rashin wadatattun sojoji ne ya sa ‘yan ta’adda da mahara ‘yan bindiga ke ci gaba da kai hare-haren ta’addanci a wasu sassan Arewacin Najeriya.
Badaru wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ci gaba da cewa duk da waɗannan ƙalubale na rashin isassun sojojin da ake samu, zaratan na Najeriya su na ci gaba da daƙile gungu-gungun ‘yan ta’adda.
Badaru ya bada labarin yadda sojojin Najeriya a kwanakin nan suka samu nasarar kakkaɓe manyan gagarman ‘yan ta’adda har su bakwai.
“Maganar gaskiya babu isassun sojoji, shi ya sa abin da ‘yan bindiga ke yi, sai su samu yankunan da babu jami’an tsaro su riƙa kai hare-hare a can. Da sun kai hari kuma sai su gudu su tsere cikin daji.”
Batun rashin wadatattun sojoji da Badaru ya yi, ba shi ne karon farko da aka tayar da wannan gagarimar matsalar ba. Saboda ko Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya sun bayyana haka a lokacin da suka amsa gayyatar Majalisar Ƙasa.
Duk da tun asali aikin sojoji shi ne kare ƙasa daga hare-hare ko farmaki daga ƙasashen waje, matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan ta sa an riƙa girke sojoji a kusan dukkan hanyoyin jihohi 36 na Najeriya da Abuja.
Gwamnatin Bola ta yi alƙawarin ɗaukar ɗimbin matasa aikin soja da sauran ɓangarorin hukumomin tsaro.
A ranar Talata, Minista Badaru ya yi tattaunawa da manema labarai, bayan ya yi jawabi ga Manyan Jami’an Sojoji na Kwas mai Lamba 46, a Babbar Kwalejin Horas da Manyan Sojoji ta Jaji, Kaduna.
Ministan wanda ya je ne a rangadin ziyara, ya yi jawabin yayin da ake gabatar da taron ƙara wa juna sani a kwalejin, kan salon daƙile mahara da ‘yan ta’adda.
Badaru ya ƙara da cewa, “Gwamnati ta maida himma sosai wajen ganin ta daƙile maharan ta’addanci, a wani tsarin inganta tsaro mai salon amfani da al’ummar yankuna.
“Mun ɗauko wannan gagarimin aiki, ɗaukar gaba-gaɗi, ta yadda za a samu nasarar kakkaɓe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga baƙi ɗaya.”
Badaru ya bada tabbacin cewa za a kakkaɓe duk wasu gungun ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.
Da ya ke rangandin duba wasu kayayyakin inganta tsaro a kwalejin, ya ce an tanadi kayan ne domin horas Da sojoji a samu zaratan musamman 2,400, waɗanda za su yi wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda kakkaɓar a-yi-ta-ta-ƙare.
Ya ce za a fara ne da horas da zarata 800 tukunna, waɗanda za su fara horaswa ɗin nan da watanni biyu.
Yayin da ya kai ziyara a Kuriga, Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya ce za a ƙwato yaran, kuma ya yi alƙawarin inganta tsaro ta hanyar sake gina ofishin ‘yan sanda a Kuriga.
Satar Mata ‘Yan Gudun Hijira 200 A Barno:
Wani munmunan labari kuma shi ne yadda rahotanni suka tabbatar da cewa ‘yan Boko Haram sun arce da mata ƙimanin 200 a Gamboru Ngala, Jihar Barno.
Sahihiyar majiya ta ce matan dukkan su ‘yan gudun hijira ne da ke zaune a sansanin gudun hijira na Gamboru, bayan hare-haren ta’addanci ya baro su daga gidajen su.
An ce Boko Haram sun kama su a cikin daji, lokacin da matan suka daji domin ɗebo itacen da za su yi girki. Wata majiya kuma ta ce sun je ne ɗebo itacen da za su sayar.
Babban Jami’in Agajin Jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke yankin, Mohammed Malik Fall, ya tabbatar da cewa ba a san takamaiman yawan matan da Boko Haram ɗin suka gudu da su ba, amma dai ya tabbatar da cewa sun kai 200.
Discussion about this post