Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa mutum 411 sun kamu da zazzabin Lassa yayin da cutar ta yi ajalin mutum 72 a jihohin 21 a kasar nan.
Hukumar ta ce alkalumar yaduwar cutar da ta fitar daga makon farko zuwa na shida a shekarar 2024.
NCDC ta ce an samu yaduwar cutar daga mutum 70 a mako na biyar wanda ya fara daga ranar biyar zuwa 12 ga Fabrairu zuwa mutum 83 a mako na shida.
Kashi 65% daga cikin mutanen da suka kamu da cutar daga jihohin Ondo, Edo da Bauchi suke sannan sauran kashi 35% daga jihohi 17.
A yawan mutanen da ake zargin sun kamu da cutar an samu raguwa a 2024 domin a shekarar mutum 2,122 ne ake zargin sun kami sannan a 2023 mutum 8,280.
Hukumar ta ce masu shekaru 21 zuwa 30 ne suka fi kamuwa da cutar sannan bana jami’an lafiya biyu sun kamu da cutar.
Rashin zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar, rashin tsaftatace muhalli na daga cikin matsalolin dake yada cutar.
Zazzabin lassa
Zazzabin lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta sannun a hankali tana ta afkawa mutane a kasar nan kusan duk shekara
Ya kan yi wahalakafin a gano cutar a jikin mutum domin yakan dauki akalla kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.
Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wadanda suka kamu da cutar sannan idan kuma ba a gaggauta zuwa asibiti ba.
Alamun kamuwa da zazzabin lassa
Ciwon Kai: Yawaita fama da ciwon kai
Zazzabi: Za a rika Jin jiki yayi nauyi kamar an jin Zazzabi.
Ciwon jiki: Jikin mutum zai rika yawan ui masa ciwo matuka. Gabobi su yi ta ciwo.
Amai: Saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum Kuma zai rika yawan yin amai.
Rashin iya cin abinci: Zazzabin lassa na hana mutum iya cin abinci.
Yawan yin bahaya: Za a yi fama da yawan shiga ban saki.
Yawaita suma: Idan hat mutum ya kamu da wannan cuta za a rika yawan sums saboda rashin lafiyar dake jikin mutum.
Jini: Za a rika zubar da jini ta wasu kafafen jiki musamman idan cutar ta fara nisa ba tare da an nemi magani ba. Hakan ya nuna cewa cutar ta fara yi wa mutum mummunar illa.
Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da zazzabin lassa
Tsaftace muhalli: A Rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wurare.
Zubar da shara: Idan aka Tara shara kada a rika zubar da shi kusa da gida a rika kaiwa can waje.
Killace Abinci da ruwan Sha: Yin haka zai taimaka wajen hana bere ko kwari shiga cikin abinci ko ruwan sha.
Dafa nama: Kafin a dafa nama kamata ya yi a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.
Tsafta: A yawaita wanke hanaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci a inci sannan idan an kammala amfani da ban daki.
Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbstsr sun nemi magani da zarar allurar da suka Yi amfani da shi a jikin wands ke dauke da cuter ya sole su.
Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake Koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyauewa waje. Kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.
Wanke gawa a cikin daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ko Kuma a inda ya kamata.
Discussion about this post