Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Makera da aka yi ranar Asabar.
Sakamakon zaben ya nuna cewa Liman dan takarar jami’iyyar APC ya samu kuri’u 18,068 inda ya kada dan takarar jami’iyyar PDP Solomon Katuka wanda ya samu kuri’u 17,404 sannan dan takarar jami’iyyar Labour party Usman Yakuti ya samu kuri’u 3,709.
Zaben ya gudana a rumbunan zabe biyar dake Mazabar Makera da suka hada da Kakuri Hausa, Television, Kakuri Gwari, Barnawa 1 da 2.
Hukumar zaben ta kuma sanar da dan takarar jami’iyyar PDP Nura Abubakar a matsayin wanda ya yi nasara a zaben Mazabar Kudan inda ya samu kuri’u 24,178.
Dan takarar jami’iyyar APC Abbas Faisal ya samu kuri 22,438 sannan dan takarar jami’iyyar Labour Party Suleiman Umar ya samu kuri’u 1,491.
Hussein Jallo na jam’iyuar PDP ya kashe zaben Mazabar Igabi da kuri’u 47,313 wanda da su ya kada dan takarar jami’iyyar APC Zyyad Ibrahim wanda ya samu kuri’u 43,915.
A karamar hukumar Chikun David Jesse na jam’iyyar APC ya lashe zaben da kuri’u 18,566 ya kada ‘yar takarar jami’iyyar PDP Maria Dogo mai kuri’u 10,903 sannan na jam’iyyar Labour party Solomon Adamu ya samu kuri’u 3,285.
Jami’in hukumar zabe farfesa Isah Bayero na jami’ar Ahmad Bello Zaria ya sanar da sakamakon zaben.
Discussion about this post