Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa a halin rugumutsin matsalar tattalin arzikin ƙasa da ake fama, da a ce shi ne shugaban ƙasa zai umarci Babban Bankin Najeriya ya bijiro da “hanyar da za a bi a hankali cikin sauƙi domin a daƙile tsadar kuɗaɗen ƙasashen ketare, musamman ma Dalar Amurka.”
Cikin wani bayani da Atiku ya watsa a shafin sa na Tiwita, wato X a ranar Lahadi, Atiku ya bijiro da wasu hanyoyin da ya ce su ne mafita ga tsallake siraɗin da tattalin arzikin Najeriya ya rufta a ciki.
Ya ce da an yi hakan to zai dakatar da faɗuwar darajar Naira. Ya ce da shi aka zaɓa shugaban ƙasa, da wannan tsarin zai bijiro da shi.
“Ganin irin halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, ƙyale Naira ta ƙwatar wa kan ta daraja a kasuwar musayar kuɗaɗe, abu ne tamkar mutum ya fito ya na kirari ya lafta wa cikin wuƙa,” inji Atiku.
“Tsarin a riƙa duba ana saran gatari shi ne zai fi dacewa. Wato a bar Naira ta ci kasuwa a kowace rana. Amma kuma CBN ya kasance shi ne mai riƙe da akalar Naira, kuma wanda makullan shiga kasuwar ke hannun sa. Domin a haka zai iya samar wa Naira darajar ta.”
CBN ya karya darajar Naira domin a samu shigowar kuɗaɗe daga hannun masu zuba jari da daga wajen.
To sai dai kuma tsarin ya ragargaza darajar Naira sosai, kuma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
Game da tsadar rayuwa, tuni dai ƙungiyoyin ƙwadago za su yi wa tsadar abinci da tsadar rayuwa zanga-zangar game-gari.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta buga gangar fita zanga-zangar nuna damuwa dangane da tsadar abinci da tsadar rayuwa har tsawon kwanaki biyu.
NLC ta shirya yin zanga-zangar a ranakun 27 da 28 ga Fabrairu, kamar yadda Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Joe Ajaero ya bayyana a ranar Juma’a, yayin wata ganawar da ya kira suka yi da manema labarai, a Hedikwatar NLC da ke Abuja.
Ajaero ya ce sun yanke shawarar tafiya zanga-zangar yajin aikin bayan cikar wa’adin da suka ba Gwamnatin Tarayya na kwanaki 14, domin ta shawo kan gagarimar matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a faɗin ƙasar nan.
Dama kuma a cikin makon jiya ne Ƙungiyar Ƙwadago ta nemi a ƙara gejin mafi ƙanƙatar albashi daga Naira 30,000 zuwa Naira miliyan 1.
Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da raɗaɗin tsadar rayuwar da ta kai har an fara yi wa yunwa zanga-zangar fito-na-fito a wasu sassan ƙasar nan, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa mai yiwuwa ƙungiyar ta nemi Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin mafi ƙanƙantar albashi daga Naira 30,000 ya koma daga daga Naira miliyan 1 zuwa sama.
Discussion about this post