Shugaba Bola Tinubu ya yanke shawarar yin amfani da shawarwarin da Kwamitin Stephen Oronsaye ya Bai wa Gwamnatin Tarayya, tun lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan.
Tinubu ya ce zai yi amfani da shawarwarin, masu ƙunshe da cewa ya kamata a rage kashe kuɗaɗen gwamnati, ta hanyar rushe wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya, waɗanda ba su da wani tasiri, da waɗanda ayyukan su ya yi kamanceceniya da na wasu ma’aikatun ko cibiyoyin.
Haka kuma a cikin shawarwarin akwai buƙatar a haɗe wasu hukumomin ko cibiyoyin a cikin wasu ma’aikatun da suka dace.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Tinubu, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka, a cikin shafin sa na Tiwita, wato X.
“Shekaru 12 bayan Kwamitin Steve Oronsaye ya miƙa wa gwamnatin tarayya rahoton da ke ƙunshe da shawarwarin rage Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Zartaswa a yau sun amince a fara rage yawan hukumomin, wasu kuma a haɗe su wuri ɗaya,” cewar Onanuga.
Za A Rushe Hukumomi Da Yawan Gaske – Tinubu:
Onanuga ya ce za a rushe hukumomin gwamnatin tarayya masu yawan gaske, wasu da dama kuma za a haɗe su wuri ɗaya, ko a haɗe hukuma ko cibiya a cikin ma’aikatar da su ke a ƙarƙashin ta.”
Haka kuma da ya ke yi wa manema labarai bayani bayan tashi taro a Fadar Shugaban Ƙasa, Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ya ce za a rushe wasu ma’aikatun, wasu kuma a haɗe su da wasu.
Ya ce amfanin yin hakan shi ne a rage yawan kashe kuɗaɗe, ba wai don a jefa ‘yan Najeriya cikin halin rashin aikin yi ba.
Idris ya ce bayanin ma’aikatun da abin zai shafa sai nan gaba ba da daɗewa ba za a bayyana sunayen su.
Ya ƙara da cewa an ma kafa kwamitin da zai shata fara amfani da rahoton na Kwamitin Oronsaye.
Kwamitin Oronsaye:
Cikin 2011 ne tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ya kafa kwamitin domin a yi wa ma’aikatu da hukumomi da cewa cibiyoyin gwamnatin tarayya garambawul, bisa jagorancin shugaban kwamiti, Steven Oronsaye, tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
A cikin rahoton kwamitin, sun fayyace cewa akwai cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya har 541.
Kwamitin ya bada shawarar a rushe Hukumomi 263 su koma 161, cibiyoyi kuma wato agency a rushe 38, wasu 58 kuma a haɗe su cikin sassan cikin ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Discussion about this post