Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ɓarkewar cutar korona da kuma bashin Naira tiriliyan 30 da Gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ci daga Babban Bankin Najeriya, CBN, su ne manyan dalilan afkawar ƙasar nan cikin raɗaɗin tsadar rayuwa da ƙangin tsadar abinci.
Akpabio, wanda ya ce gwamnatin tarayya da sanatocin Najeriya su na bakin ƙoƙarin su domin magance wannan gagarimar matsala, ya ce duk wani surutu da za a tsaya ana yi a yanzu, to Turanci ne kawai, abin da talaka ke buƙata shi ne abincin da zai ci.
Sai dai kuma ya ce zanga-zangar da ake yi a wasu jihohi wasu marasa kishin Gwamnatin Tarayya da yi mata zagon-ƙasa ne ke ɗaukar nauyin shirya ta.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin ƙoƙarin ganin abinci ya samu sauƙi da rangwamen farashi.
Da ya koma kan ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi, Akpabio ya ce, “kowane gwamna ya karɓi Naira biliyan 30 daga Tarayya, domin raba wa talakawa abinci.”
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi iƙirarin cewa ya samu labarin da bai tabbatar ba cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa kowane gwamna kuɗin kishi-kishi, har kowa ya karɓi Naira biliyan 30, domin su rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa.
Akpabio ya bayyana cewa an ciri kuɗin ne daga Asusun Gwamnatin Tarayya an raba wa gwamnonin domin a rage tsadar kayan abinci da tsadar rayuwa a kowane jiha.
Akpabio ya bayyana haka a zaman Majalisar Dattawa na ranar Talata, inda ya ce labarin da ya zo masa na nuni da cewa an ba su kason farko ba tun yau ba, sannan kuma gwamnonin dai sun sake karɓar Naira biliyan 30 kowanen su daga Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).
“Tilas ta kama zan bayyana cewa kowace jiha ta karɓi Naira biliyan 30 cikin ‘yan watannin nan daga Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).
“Waɗannan kuɗaɗe da aka ba su, ba su cikin haƙƙin kuɗaɗen su da gwamnatin tarayya ke ba su na duk ƙarshen wata daga Asusun Gwamnatin Tarayya. An ba su ne domin su rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci,” cewar Akpabio.
Akpabio ya shawarci gwamnoni su yi amfani da kuɗaɗen ta inda ya dace, kuma ta hanyar amfana su ga talakawa da marasa galihu, domin rage masu tsadar rayuwa.
“Mun yi amanna da cewa matsawar gwamnoni za su yi amfani da kuɗaɗen ta hanyar wadatar da abinci, to za a samu sauƙi sosai.
“Gwamnatin jiha na da jan aiki a kan ta. Ita ce kusa da jama’a. Ba na so na ce ƙananan hukumomi ne suka fi kusanci da jama’a, domin kowace ƙaramar hukuma a yanzu ƙarƙashin gwamna take.
“Amma dai na yi amanna cewa idan gwamnatin jiha za ta yi abin da ya kamata, to sai ta jawo ƙananan hukumomi wajen raba kayan abincin ga mabuƙata.” Inji Akpabio.
Akpabio ya yi wannan iƙirarin daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da ɗanɗana raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci.
Tuni ake ta samun rahotannin zanga-zanga a jihohi daban-daban.
Ita kuwa Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NL ), ta sanar cewa a ranakun 27 da 28 ga Fabrairu za a yi zanga-zangar game-gari a faɗin ƙasar nan.
Discussion about this post