Wata sabuwar amarya mai suna Aisha Aliyu da ke kauyen Nasarawa a Karamar Hukumar Lapai a Jihar Neja, ta yi wa angonta Idris Ahmadu yankan rago.
Mazauna yankin sun tabbatar wa Aminiya abin da ya faru inda suka ce amaryar ta kashe mijinta da misalin karfe 1 na dare.
Ma’auratan sun yi aure ne a ranar 31 ga watan Disambar 2023.
Wata majiya ta ce ma’auratan sun samu matsala da yammacin ranar Lahadi.
Majiyar ta ce an sassanta ma’auratan kafin dare amma cikin dare sai mahaifiyar angon ta ji danta na ihun yana neman dauki.
“Lokacin da mahaifiyarsa ta fito tare da wasu da ke zaune a gidan, sai suka samu angon kwance cikin jini. Ahmadu ya yi kokarin gudu daga dakin amma sai ya fadi a bakin kofa sannan har yanzu ba mu san inda amaryar ta shiga ba.”
Majiyar ta ce amaryar ta fara daɓa wa Ahmadu wuka a kirji sannan ta yi masa yankan rago.
Ma’auratan dai sun kwashe shekaru suna soyayya har zuwa lokacin da aka sa ranar bikinsu amma daga baya amaryar ta canja ra’ayi.
“An warware matsalar sannan sun ci gaba da soyayya har aka daura musu aure. Ashe ba a san cewa amaryar na da shirin da ta kulla a zuciyarta ba.
“Aisha ta fara soyayya da Ahmadu tun suna makaranta inda sai gab da za a dauran musu aure ta ce bata yi cewa ta samu Sabon saurayin da take so
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Wasiu Abiodun ya tabbatar da aukuwar lamarin sai dai ya ce kafin jami’an tsaro su isa gidan Aisha ta gudu.
Abiodun ya ce jami’an tsaron sun fara farautar Aisha domin kamo ta.
Discussion about this post