Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
‘Yan uwana ‘yan Najeriya! Da farko ya kamata mu sani, tabbas, bayan addini, abinci yana daga cikin abubuwa na asali (basic requirements), wadanda dan Adam dole yake bukata domin ya rayu a bayan kasa. Dalilin haka yasa, duk wani abu da zai kawo wa dan Adam barazana wurin samun abincin nan, to wannan abu ko menene shi, zai zama babban makiyi ga dan Adam; kuma wannan abu zai zama barazana kenan ga wanzuwar ‘yan Adam a bayan kasa.
Kuma da zarar an samu wannan a cikin ko wace irin al’ummah, to maganar samun zaman lafiya a cikin wannan al’ummar, wallahi sai dai su ji labarinsa a cikin mafarki, amma ba zai samu ba. Wannan sunnah ce ta Allah Subhanahu wa Ta’ala!
Don haka ba wani abun mamaki bane, don an samu tashe-tashen hankula, tarzoma, zanga-zanga, ko wani abu mai kama da haka, a cikin wannan al’ummah wadda Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi wa arziki kala-kala, iri-iri a cikin karkashin kasa, amma aka wayi gari sai dai kawai suji ana ta lissafin tiriliyoyin kudade da sunan su. Al’ummar da suna ji suna gani shuwagabannin su suke ta almubazzaranci da dukiya a banza.
Duk wanda ya karanta labari na ra’ayin jaridar Premium Times, game da irin kudade da shuwagabannin mu suke ci, da sunan abinci, tafiye-tafiye, sutura, magani, tarurruka, motoci, kayan kyale-kyali da sauransu, wallahi hankalinsa zai tashi, zaya rude, kuma ya dimauce.
Domin zaka ji cewa, anya da gaske ake yi a wannan kasa tamu kuwa???
Allah ya sawwake, yayi muna mafita, amin.
Yaku ‘yan uwana ‘yan Najeriya! Lallai Annabin mu, Annabin Rahama, Annabi Muhammad (SAW) ya hana shuwagabanni su tsanantawa talakawansu; ya hana su yaudari mabiyansu ko su ha’ince su, ko su zalunce su, ko suci amanar su, ko su cutar da su ta kowane hali. Kamar yadda mu ma mabiyan su, ya umurce mu da mu fada wa shugabanninmu gaskiya. Ya hana mu mu yaudare su. Ya hana mu ha’ince su. Ya hana muci amanar su. Ya hana muyi masu karya. Ya hana muci mutuncinsu ko mu zage su. Ya hana mu cuce su, ko mu boye masu gaskiyar ainihin abun da yake faruwa a kasar da suke shugabanci, ko game da matsalolin talakawan su. Ya hana muyi masu fadanci na karya, na cin amana, da banbadanci don kawai su so mu, ko don neman wani abu daga hannunsu. Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) kamar haka:
عن أَبي يَعْلَى مَعْقِل بن يَسَارٍ قَالَ: سمعتُ رسولَ اللَّه ﷺ يقول: مَا مِن عبدٍ يسترعِيهِ اللَّهُ رعيَّةً، يَمُوتُ يومَ يَموتُ وهُوَ غَاشٌّ لِرَعِيَّتِهِ؛ إلَّا حَرَّمَ اللَّهُ علَيهِ الجَنَّةَ.” متفقٌ عليه
وفي روايةٍ: “فَلَم يَحُطْهَا بِنُصْحهِ لَمْ يجِد رَائِحَةَ الجَنَّة.”
وفي روايةٍ لمسلم: “مَا مِن أَمِيرٍ يَلِي أُمورَ المُسلِمينَ، ثُمَّ لا يَجْهَدُ لَهُم ويَنْصَحُ لهُم؛ إلَّا لَم يَدخُل مَعَهُمُ الجَنَّةَ.”
Ma’ana:
An karbo daga Abi Ya’ala, Ma’aqil Dan Yasar, yace: “Naji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Babu wani mutum ko wani shugaba, da Allah zai dora wa wani Shugabanci, har ya kasance yana ha’intar talakawan sa; face sai Allah ya haramta masa shiga Aljannah.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]
A wata ruwaya, Annabi (SAW) yace: “Duk wanda Allah ya ba shugabanci, sai bai yi kokari wurin yin nasiha ga talakawan sa ba, bai yi kokarin dawo dasu kan hanya, tare da kokarin kyautata masu ba, to ko kamshin Aljannah ba zai taba ji ba, (balle ya shige ta).”
A wata ruwaya ta Muslim:
Annabi (SAW) yace: “Babu wani shugaba da zai shugabanci musulmi, sannan ya kasance ba yi kokari wurin tabbatar da maslahar su ba, ko gyara lamurran su ba; face sai Allah ya hana shi shiga Aljannah tare da su (Ma’ana, su zasu shiga Aljannah, amma shi a hana shi shiga).”
Sannan Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) kamar haka:
عن ابن عمر رضي اللَّه عنهما قَالَ: سمِعتُ رسولَ اللَّه ﷺ يقول: كُلُّكُم راعٍ، وكُلُّكُمْ مسؤولٌ عَنْ رعِيَّتِهِ: الإمامُ راعٍ ومَسْؤُولٌ عَنْ رعِيَّتِهِ، والرَّجُلُ رَاعٍ في أهلِهِ وَمسؤولٌ عَنْ رَعِيَّتِهِ، وَالمَرأَةُ راعيةٌ في بيتِ زَوجها وَمسؤولةٌ عَنْ رعِيَّتِها، والخَادِمُ رَاعٍ في مَالِ سَيِّدِهِ وَمَسؤُولٌ عَنْ رَعِيَّتِهِ، وكُلُّكُم رَاعٍ ومسؤُولٌ عَنْ رعِيَّتِهِ.” متفقٌ عَلَيْهِ
Ma’ana:
“An karbo daga Abi Hurairah (RA) yace: Naji Manzon Allah (SAW) yana cewa: ” Dukkanin ku masu kiwo ne, kuma duk sai an tambaye ku game da abun da aka baku kiwo; Shugaba mai kiwo ne, za’a tambaye shi game da talakawan da aka bashi kiwo! Ko wane mutum mai kiwo ne akan iyalinsa, kuma za’a tambayeshi game da su! Ko wace mace mai kiwo ce a gidan mijinta, kuma za’a tambaye ta game da wannan kiwo, na yadda ta zauna da shi! Sannan yaron gida, ko yaron shago, ko yaron kasuwa, kai ko wane irin hadimi, dukkaninsu masu kiwo ne game da dukiyar mai gidansu, kuma za’a tambaye su akan ta! Kai dukkanin ku masu kiwo ne, kuma duk za’a tambaye ku akan kiwon da aka baku.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]
Kuma lallai duk shugaban da yanayin shugabancin sa ya tsanantawa al’ummah, to wannan shugaban ya sani, shima zai hadu da takura da kuma tsanani daga wurin Allah. Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) kamar haka:
عن عائشة رضي الله عنها قَالَتْ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ ﷺ يقُولُ في بيتي هَذَا: اللَّهُمَّ مَنْ وَلِيَ مِنْ أَمْرِ أُمَّتي شَيْئًا فَشَقَّ عَلَيْهِمْ فاشْقُقْ عَلَيْهِ، وَمَنْ وَلِيَ مِنْ أَمْرِ أُمَّتِي شَيْئًا فَرَفَقَ بِهِمْ فَارْفُقْ بِهِ.” رواه مسلم
An karbo daga Aisha (RA) tace: “Naji Manzon Allah (SAW), wata rana, yana fada a cikin wannan daki nawa, yana addu’a, yana rokon Allah, yana cewa: “Ya Allah! Duk wanda ka ba wa shugabanci kowane iri ne a cikin wannan al’ummah, kuma ya kuntata masu, Ya Allah, shi ma ka kuntata masa, ka tsananta masa! Haka nan Ya Allah, duk wanda ka ba wa wani shugabanci daga cikin al’ummah ta, sai ya saukaka wa al’ummah, shi ma Ya Allah, ka saukaka masa, ka tausaya masa.” [Muslim ne ya ruwaito shi]
‘Yan uwana ‘yan Najeriya! Tabbas wasu manyan sauye-sauye guda biyu ko fiye da haka, wadanda mai girma Shugaban kasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu yayi a gwamnatinsa; sauye-sauyen da yayi su ne da kyakkyawar niyyah, da manufa mai kyau, da tunanin zasu taimaki kasar nan da ‘yan kasa baki daya, sauye-sauyen da suka haɗa da cire tallafin man fetur da kuma cewa a bar kasuwa ta tantance darajar kudin kasar mu, wato naira, hakika sune suka kara kawowa talakawan Najeriya tsanani, yunwa, wahala da rashin tabbas; bayan rufe iyakokin kasa (boarder) da gwamnatin da ta gabata ta Shugaba Buhari tayi!
Saboda haka muna kira da don Allah a sake duba wadannan tsare-tsare, ya kai mai girma Shugaban Najeriya, Alhaji Bola Ahmed Tinubu!
Kuma hakika, ko shakka babu, wadannan matsaloli na yunwa, talauci, faduwar darajar Naira, hauhawar farashin kayan abinci da kayayyakin masarufi da sauran kayayyaki a kasar mu Najeriya, idan bamu yi hankali ba, idan ba mu bi sannu ba, idan ba’a dauki matakin da ya kamata ba, wallahi yana iya haifar muna da mummunar tarzoma da zanga-zanga da tashin hankali a tsakanin al’ummah.
Kamar dai yadda kuke ji, kuma kuke gani, tuni aka fara zanga-zanga a wasu jihohi na sassan kasar nan, saboda irin yadda yunwa da talauci da tsadar rayuwa suke ta karuwa kullun a kasar nan; zanga-zanga ta faro daga jihar Neja, yau gashi tana ta kara yaduwa zuwa wasu jihohi kamar, jihohin Filato, Kano, Sokoto, Osun, Oyo, Legas, Edo, Ondo, Kogi da Birnin Fatakwal.
Ya ku jama’ah! Wallahi ko jahili, wanda bai taba zuwa koi’na yayi karatu ba, yasan da cewa akwai yiwuwar a sami karin tarzoma da tashe-tashen hankula a tsakanin al’ummah, saboda rashin muhimman abubuwan nan na rayuwa; abinci, matsuguni da tufafi, wanda mafi muhimmanci a cikinsu, kuma mafi girma shine abinci, wanda dan Adam yana iya haukacewa, idon sa su rufe saboda rashinsa. Domin babu wanda zai iya rayuwa ba tare da ya samu abinci ba, ta ko wace hanya ce kuwa. Kuma yanzu hanyar da ‘yan Nijeriya suka dosa kenan. Allah ya sawwake, amin.
Eh, duk da cewa mun san duniya baki daya ce take cikin wannan radadin, ba wai Najeriya ba ce kawai. Amma wasu tsare-tsare na gwamnati a Najeriya, sun kara ta’azzara matsalar! Don haka ya zama wajibi gwamnati tayi dukkan mai yiwuwa domin kaucewa fuskantar tarzoma, zanga-zanga da barkewar tashe-tashen hankula. Domin shi mai jin yunwa mutum ne da tabbas yake cikin tsananin fushi da damuwa mai girma (Hungry man is an angry man). Kuma babu wani lallashin da zaka yi masa ya saurare ka, har ya yarda da kai. Iyakar abunda zaka yi masa ya saurare ka shine, ka samar masa da mafita kawai.
Koda yake abin farin ciki, kuma magana ta adalci shine, a gaskiya ita ma gwamnati ba ta yi bacci ba, tana iya kokarin ta, ta tashi tsaye wajen ganin an magance wadannan matsalolin, tare da samar da matakan kawo sauki a duk fadin kasar nan. Allah ya taimakesu, yasa masu hannu, ya kawo muna sauki, amin.
Amma dai duk da haka, ba zamu gushe ba a koda yaushe, wurin kira ga shugabanni a dukkan matakan gwamnati da su kara kaimi, su gaggauta daukar matakan kawo wa mutane saukin matsin rayuwar da suke fuskanta domin kaucewa fushin Allah (SWT), da kaucewa tashin hankali, tarzoma da mummunar zanga-zanga!
Har ga shi wannan halin matsi da tsadar rayuwa ya tilasta ‘yan Najeriya gudanar da zanga-zanga a wasu jihohi. Saboda halin da mutate suke ciki ya wuce duk yadda ake tunani. Lamarin a halin yanzu ya kai matsayin Inna lillahi wa Inna Ilaihi Raji’uun!
Babu wani bangare na rayuwar al’ummah da basu dandana wannan halin da ake ciki. Don haka muna kira ga gwamnatoci da su samar wa al’ummah mafita domin mu zauna lafiya.
Kusan yanzu kowa ka gani a hanya yana tafiya, wallahi yana bukatar taimako.
Wannan mummunan halin kunci da mutane suke ciki, kullun sai kara ta’azzara yake yi, kuma wani lokacin sakamakon munanan halayenmu da rashin jinkai da tausayin junanmu, a ko wane mataki na kasa zuwa sama.
Ya kamata gwamnati ta saurari koke-koken al’ummah da koken-koken talakawanta, ta dawo da tallafin man fetur da ta cire, kasancewar man fetur ya shafi dukkan bangarorin rayuwar al’ummah, kuma janye wannan tallafi tabbas ya taimaka wurin haifar da tsadar rayuwa.
Kuma ya kamata gwamnati ta bude iyakokin kasar nan da aka rufe a baya, in dai har domin al’ummah suke mulki.
Kuma gashi darajar naira na kara karyewa a kullum, saboda wadannan tsare-tsare da gwamnati ke bi na tattalin arziki.
Kuma idan har gwamnati ba ta dauki matakin kawo wa al’ummah saukin rayuwa ba, to lallai za su gamu da fushin Allah (SWT) da kuma fushin ‘yan kasa. Kuma sannan su sani, zasu iya fuskantar mummunan kalubale, musamman a lokacin da su ma suke bukatar goyon bayan ‘yan kasar. Wannan shine gaskiyar magana.
Wasu daga cikin sassan malamai suna cewa:
“Allah yana iya kwace mulki daga hannun wadanda ba zasu iya taimakon mutane ba, ya ba wadanda za su taimaka wa mutane.”
Sannan kuma ya zama wajibi a cire duk wani irin tunani na siyasa wajen bayar da dukkan wani taimako ko kuma tallafi, domin idan ana maganar matsin rayuwa da yunwa, to babu banbanci tsakanin dan APC ko dan PDP, kai ko dan wace jam’iyyah ce.
Muna roko da kira ga gwamnatin mai girma Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ta yiwa Allah ta duba halin da al’ummar kasar nan suka shiga.
Domin gaskiyar magana, ana yunwa a kusan ko ina a sassan kasar nan. Ya kamata a bude baitul-malin kasar nan, domin a taimakawa bayin Allah.
Ni ban ga amfanin a tara kudi da nufin yin ayyukan more rayuwa ba. Ko ayi ta ayukkan gine-ginen hanyoyi da tituna, da wasu kawace-kawace, da gyare-gyare, alhali al’ummar kasa suna ta mutuwa saboda yunwa.
Don Allah muna aika sako zuwa ga mai girma Shugaban kasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, da gwamnoni, da mawadata da ‘yan kasuwa, da suyi kokari don Allah, su duba irin halin da al’ummah suke ciki a kasar nan.
Muna bayar da shawara tsakaninmu da Allah, zuwa ga gwamnati, da ta raba abinci ga ‘yan kasa, domin a samu saukin yunwa da talauci da suka yi katutu a ko wane lungu da sako na kasar nan!
Tsakanina da Allah, al’ummah suna cikin masifa da talauci da yunwa, fiye da yadda kake tsammani. Kuma duk wanda ya fada maku cewa babu wannan, to baya tsoron Allah, kuma ba masoyinku bane, ko kuma matsalar ba ta iso gidansu ba.
Da wannan ne muke kira ga mai girma Shugaban kasar Najeriya, Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da dukkanin shugabanni, da su sani, tabbas mutane suna cikin yunwa. Kuma mai girma Shugaban kasa ya sani, babu lokacin da ya kamata gwamnatinsa ta taimaka kamar irin wannan lokaci.
Don Allah a bude baitul-malin gwamnati, a debo dukiya, a saye abinci, idan akwai abincin a ajiye a fito da shi, a taimakawa bayin Allah!
A halin yanzu, talakawan Najeriya babu abun da suke nema illa samun saukin wannan halin tsananin da suke ciki.
Don Allah ku kyale talaka da maganar gine-ginen hanyoyi da sauransu a halin yanzu, ku fuskanci wannan muhimmin al’amari, na saukakawa bayin Allah wannan halin tsananin rayuwa da suka samu kan su a ciki!
Ya kamata mai girma Shugaban kasa, da gwamnoni, da dukkanin shugabanni da masu hannu da shuni su sani, wallahi idan kuka raba tirelolin shinkafa, masara, gero, dawa, taliya, sukari da garin tuwo, gwamnatin nan zata samu albarka. Allah zai tausaya maku, talakawa zasu so ku fiye da yadda kuke tsammani!
Idan kuka yi haka, za’a dauki shekaru masu yawa ana tunawa da ku da kuma gwamnatocinku, za’a yi maku addu’o’i masu kyau.
Da yawa, akwai kasashen da ba su kai kasar mu Najeriya arziki ba, amma al’ummarta suna rayuwa cikin sauki.
Don Allah menene amfanin tara kudi da ake yi bayan an cire tallafin mai?
Ina masu hali? Ina mawadata? Ina ‘yan kasuwa? Don Allah kuma ku rika taimakawa marasa karfi. Ku sani, rowa fa zata iya kara jefa kasar nan cikin karin bala’i. Bai kamata Musulmi ko wani mutumin kirki ya zama marowaci ba!
Koken-koken yunwa da talauci sun yawaita a kasar nan. Cin abinci ya gagari mafi yawan marasa karfi a kasar nan.
Adadin marasa aikin yi a kasar nan ya karu zuwa kashi biyar cikin 100, kuma a daidai wannan lokacin da ake fama da wannan irin matsalar tsadar rayuwa, bayan da gwamnati ta cire tallafin man fetur.
Ya kamata gwamnatin mai girma Bola Ahmed Tinubu su sake duba tsaren-tsaren da suka yi, wadanda suka jawo karin talauci da tsadar rayuwa a kasar nan.
A yau rayuwa tayi tsada, talakawa sun ƙuntata, masu ɗan rufin asirin ma dukiyar wasunsu ta zagwanye, talakan da yake iya ci sau uku a gidansa ada, yanzu ya dawo ci sau biyu ko sau ɗaya. Wani ma baya iya ci.
Wasu daga cikin masu mulkinmu da manyan ‘yan kasuwanninmu sun takure jama’ah, ta yadda motsi mai kyau ma mutum baya iya yi. Masu mulki kansu kawai suka sani, burinsu kawai talakawa su zaɓesu, amma su basu wahala bayan sun ci zaben. ‘Yan kasuwa kuma da yawansu burinsu shine su sayi kaya su ajiye, su boye, sai lokacin tsadarsa su fito dashi su saidawa talakawa da tsada. Duk da hanin da Allah da Manzonsa (SAW) suka yi akan hakan.
Yawan ayukkan saɓonmu ga mahaliccinmu Allah, da kuma rashin tausayi daga shugabannimu, sun sanya Allah Subhanahu wa ta’ala ya jarabemu da tsadar rayuwa, wanda har ta kai ta kawo ma wasu gidajen suna kwana da yunwa, wasu gidajen da suke iya ci sau uku a rana a can baya, yanzu sun dawo bai fi sau ɗaya ko sau biyu suke iya ɗora girki ba. Haƙiƙa wannan lamarin yana buƙatar tashi tsaye, domin yin hobbasa, da komawa ga Allah da addu’o’i, tare da yawaita tuba zuwa ga Allah Madaukaki, ko ya tausaya muna!
Ya kamata dukkaninmu mu sani, kuma mu fahimci cewa, lallai zaman lafiya, da samun cikakken tsaro, da kwanciyar hankali, da samar da ci gaba da walwala, duk suna da alaka da gusar da yunwa, talauci da fatara cikin al’ummah. Matukar al’ummah suna cikin yunwa, talauci da fatara, wallahi babu wani abu da zaka fada masu na cewa wai su zauna lafiya, kar suyi zanga-zanga, kar su tada hankali, kar suyi hayaniya, har su saurare ka.
Wannan ita ce tsantsar gaskiyar da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya umurce mu da mu fada maku, kuma da ikon Allah ba zamu ha’ince ku ko mu yaudare ku, ko muyi maku karya ba!
Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa:
“Saboda sabon kuraishawa. Sabonsu na tafiyar hunturu da ta bazara. Saboda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (na Ka’abah); wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga tsoro.” [Suratul Kuraish, surah ta 106]
Sannan daga karshe, Ya ku ‘yan Najeriya! Ku sani, lallai ina yi maku kashedi game da Allah, ku kiyayi Allah, hakika Allah yayi maku baiwa da ni’imah, tun da har ya sanya ku cikin wadanda suka riski wannan wata na Sha’aban cikin koshin lafiya da karfi da alkhairi. Kuma ga wata mai cike da tarin albarka na Ramalan yana zuwa. Don haka ku kara godiya ga Allah mai girma da daukaka a bisa wannan ni’imar da yayi maku. Ku kyautatawa kawunan ku, kuma ku kyautatawa bayin Allah, ta hanyar yawaita azumi a wannan wata na Sha’aban, da shiryawa domin zuwan watan Ramalan, da kuma zage damtse wurin ciyar da bayin Allah a cikin watan Ramalan, la’alla Allah ya sanyaku cikin wadanda zasu samu Aljannah, dalilin azumtar wannan watan da kuka yi da kuma taimakawa bayin Allah, kuma ya ‘yantar daku daga azabar wuta.
Ya ku bayin Allah ina yi maku gargadi da kashedi, game da Allah, a bisa wannan ganimar da ya baku, kada kuyi sakaci da ita, kada kuyi kasala a cikinta, kuyi rige-rige a cikinta wurin ayukkan alkhairi. Ku sani, dukkan wani abun sayarwa muhimmi, to yana da matukar tsada, kuma hakika abun sayarwar Allah shine aljannah, kuma tabbas kudin sayenta da ake nema a wurinku kadan ne yaku bayin Allah masu girma!
Allah yasa mu dace, amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, shine ya rubuto, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post