‘Yan bindiga sun kashe mutum Dagacin ‘Yar Nasarawa cikin Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.
Mamacin mai suna Haruna Wakili, an bindige shi tare da wasu mutum biyar, sannan kuma aka ƙone motoci da kantina kayan masarufi ga gidaje.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilin mu cewa maharan sun gudu da mutum 38, waɗanda suka haɗa da mata da ƙananan yara, kuma suka ji wa mutum 10 raunuka.
“Sun banka wa gidaje shida da motocin haya takwas wuta, da kuma kantina.”
Ƙauyen da lamarin ya faru ya na kusa da Sansanin Zaratan Sojojin ‘Army Super Camp’, waɗanda aka girke tazarar ƙasa da kilomita biyar a garin Faskari.
Wannan mumnunan al’amari ya faru a ranar Litinin. Sansanin sojojin dai an kafa shi ne zamanin tsohon Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Janar Tukur Buratai, cikin 2018.
“Maharan sun shigo a shirye. Domin Ni dai ban taɓa ganin irin wannan dandazon ‘yan bindiga irin waɗannan ba,” cewar wani mazaunin ƙauyen mai suna Auwal Liman.
Ya shaida wa wakilin mu cewa gudu ya yi ya shige cikin daji lokacin da aka kai masu harin.
“Ina gudu ‘yan bindiga na harbo harsasai kan-mai-uwa-da-wabi. A dai lokacin ne kuma wasu ‘yan bindigar kuma suka riƙa banka wa gidaje da motoci wuta.
Maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 11 na dare, kuma suka tare mashigar garin, don ma kada sojoji ko ‘Yan Sa-kai su kai ɗauki.
Liman ya shaida wa wakilin mu cewa an rufe gawarwakin mutum shida ɗin da aka kashe wayewar garin yau Talata.
“A yau dai mun bani mun lalace. Ba mu iya zuwa gonakin mu. Idan muka zauna gida ba mu fita zuwa kasuwa, sai ‘yan bindiga su biyo mu har gida su na kashe mu.”
Wani mazaunin garin mai suna Abdullahi Adamu, ya shaida wa wakilin mu cewa maharan ba su da imani ko kaɗan. Sun ɗauki ƙaramin yaro suka saka shi cikin ɗaki, suka banka wa ɗakin wuta. Kuma suka yi wa wani dattijo yankan-rago.”
Adamu ya ce shi tsere wa ya yi ya hau wani tsauni ya ɓoye, bai sauko ba sai da jijjifin safiya.
Ya ce ya daina tunanin kai masu wani agajin tsaron lafiyar su daga gwamnati ko jami’an tsaro.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Abubakar Sadik Aliyu ya tabbatar da kai mumnunan farmakin.
Discussion about this post