Iyalan wani mutum da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi sun yi zargin cewa Jami’in ‘Yan Sanda na Mpape da ke Abuja, ya nemi su biya shi Naira 50,000 domin a gano daidai wurin da ake tsare da maigidan ta, ta hanyar yin amfani da na’urorin zamani.
Su dai iyalan sun je Ofishin ‘Yan Sanda na Mpape ne sun kai rahoto, bayan an yi garkuwa da maigidan, wanda ya bar gida da niyyar zuwa Legas.
An sace Alfred Ahon a ranar 1 ga Fabrairu, a Mpape, kusa da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Matar sa mai suna Senami da wata maƙauciyar ta, sun je Ofishin DCO na Mpape, inda ogan na su ya nemi su ba shi kuɗin.
“Mun je Ofishin DCO na Mpape, domin su taimaka su gano inda ake tsare da maigida na, ta hanyar neman lambar sa. Amma abin ka da mai hali, an ce ba ya barin halin sa. Sai suka ce sai na ba su kuɗi.
“DCO ɗin ne da kan sa ya nemi na biya shi Naira 50,000 domin gano lambar,” inji matar Ahon.
Sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ɗan sandan ya ce ya na buƙatar kuɗin domin ya samu jami’an SSS, su ma ya ba su hasafi, saboda su ne ke sa na’urar da za a iya gano inda aka tsare mijin, ta hanyar yin amfani da na’urar ‘tracker’.
“Sun faɗa mana cewa su ‘yan sandan wai ba su da na’urar bincike, sai jami’an SSS ke da ita. To su ɗin ma wai sai an ɗan ba su wani abu,” inji matar.
Kwanaki 16 bayan an yi garkuwa da Ahon, har yau ba a sake shi ba, kuma ‘yan sanda ba su yi komai a kai ba.
Su kuma masu garkuwa sun yi barazanar kashe mutumin idan matar sa ba ta kai masu Naira miliyan 100 ba, daga nan zuwa ranar Asabar.
Ahon ya bar gida da niyyar zuwa ganin ‘ya’yan sa waɗanda ba su daɗe da shiga jami’a ba a Legas.
Ahon tsohon ma’aikacin Hukumar NIPC ne da bai daɗe da yin ritaya daga aiki ba. Amma ya ci gaba da aiki a matsayin na kwantiragi, domin ya samu ya ciyar da iyalin sa, kuma ya ci gaba da biyan kuɗin makarantar ‘ya’yan sa biyu.
Ita kan ta matar ta sa ba ta da lafiya a ranar da ya fita aka sace shi. Domin ko rakiya ba ta iya fita ta yi masa ba zuwa inda zai hau mota zuwa tasha.
Matar sa ta yi zargin ‘yan ‘One Chance’ ne suka sace shi a cikin mota a lokacin da ya bar gida kafin a kai tashar Jabi.
An yi ta tattauna wannan batu a soshiyal midiya, har lamarin ya yi tsami sosai.
Matar dai ta ce sai ranar Lahadi da rana ‘yan bindiga su ka kira ta, suka ce sun yi garkuwa da mijin ta, amma su na buƙatar Naira miliyan 100 kafin su sake shi.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan FCT Abuja, Josephine Adeh, ta shaida wa wakilin mu cewa ta na cikin wani taro, za ta kira idan ta fito. Amma dai har yau ba ta kira ba.
Discussion about this post