Kungiyar likitocin zuciya, sun gargaɗi ƴan’Najeriya su yi kallon kwallon kafa da lura kada a samu bugawar zuciya.
Idan ba a manta ba, a cikin makon jiya yayin da Najeriya ta buga wasan kusa da karshe tsakaninta da Bafana Bafana na Afirka ta Kudu wasu yan Najeriya sun yi sallama da duniya.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da Cairo Ojougboh, wanda tsohon ɗan majalisa ne, sai kuma Ayuba na jami’ar jihar Kwara sai kuma Osondu Nwoye wanda ɗan’Najeriya ne mazaunin kasar Cote D’Voire duk sun yi sallama da duniya.
NCS ta yi kira ga masu fama da ciwon zuciya, da suka haɗa da hawan jini da dai sauransu da su bi a hankali a lokacin da suke kallon kwallon kwallo.
Rahotanni da yawa sun nuna cewa yawan kiba, busa sigari, shaye-shayen ƙwayoyi, shan barasa, da rashin motsa jiki na kawo matsaloli irin haka.
Don aka ba da shawarar yin gwaji a matsayin hanya ɗaya tilo mai inganci don ganowa da wuri da kulawa da ya dace da rigakafin mutuwar farɗɗaya tsakanin jama’a.
“Mutuwar wadannan ’yan Najeriya ya zama darasi ne ga dukkan mu da lallai mu yi taka-tsan-tsan game da lafiyar zuciyarmu.
Mu rika yin kaffa-kaffada abubuwan da za su riƙa harzuƙa mu suna tada mana da hankali kwarai da bamu tsoro faraɗɗaya domin gujewa samun matsala a zuciyar mu ko kuma bugawar zuciya.
Discussion about this post