Shugaba Bola Tinubu ya yanke shawarar yin amfani da shawarwarin da Kwamitin Stephen Oronsaye ya Bai wa Gwamnatin Tarayya, tun lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan.
Tinubu ya ce zai yi amfani da shawarwarin, masu ƙunshe da cewa ya kamata a rage kashe kuɗaɗen gwamnati, ta hanyar rushe wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya, waɗanda ba su da wani tasiri, da waɗanda ayyukan su ya yi kamanceceniya da na wasu ma’aikatun ko cibiyoyin.
Haka kuma a cikin shawarwarin akwai buƙatar a haɗe wasu hukumomin ko cibiyoyin a cikin wasu ma’aikatun da suka dace.
Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya bayyana cewa akwai wasu ma’aikatu da dama da za haɗe su wuri ɗaya, sannan wasu kuma za a rushe su.
Ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati ranar Litinin.
” kamar Radiyo Najeriya, za a haɗe ta da Muryar Najeriya su zamama’aikata ɗaya kawai tunda duk daia abu daya duke yi. sannan kuma da wasu ma’aikatun da dama.
Discussion about this post