Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin ta na nan za ta bijiro da gagarimin shirin wadata yara da ingantaccen ilmi a faɗin ƙasar nan, domin yin hakan ya taimaka a daƙile matsalar tsaro a ƙasa baki ɗaya.
Tinubu ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi wajen taron rantsar da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda aka rantsar a zango na biyu ranar Talata.
A jawabin sa, Tinubu ya ce kafin zuwan Hope Uzodinma zuwa Imo ya na da matuƙar wahala, saboda tashe-tashen hankula.
Da ya ke warware yadda za’a shawo kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan, Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta yi amfani da damar da ilmi wajen daƙile matsalar rikice-rikicen da suka dabaibaye ƙasar nan.
“Ilmi shi ne rigakafi, kandagarki kuma maganin da za’a sha a kasar da matsalar tsaro, musamman faɗace-faɗace da ta’adanci a faɗin ƙasar nan.”
Tinubu ya ce ko yunwa ita ma babban makamin ta shi ne ilmi.
“Mun bada himma ƙwarai wajen ganin mun kawo dawwamammen zaman lafiya a faɗin ƙasar nan. Za mu bada fifiko wajen ilmantar da yara.
“A ƙarƙashin wannan shiri, za mu rungumi malaman makarantu sosai wajen gudanar da shirin.
“Ilmi ne ya kai ni ga wannan matsayi, tare da addu’o’in ku da kuma goyon bayan ku. Idan babu ilmi, babu abin da ɗan Adam zai iya cimma, kuma babu abin da za a iya yi domin a cimma ɗan Adam ya kai gacin wani tasiri a rayuwa.
Najeriya na fuskantar matsalar tsaro wadda kusan matasa ne a sahun gaban tayar da fitintinun ta’addanci, garkuwa da mutane da tada ƙayar bayan da ‘yan IPOB ke yi, masu rajin ɓallewa su kafa Biafra.
Tsawon shekaru kusan 12 kenan Najeriya na fama da kashe-kashe, garkuwa da mutane, Boko Haram da tarwatsa mazauna yankunan karkara daga garuruwan su.
Discussion about this post