Kiran goron gayyatar da Shugaban Riƙon APC, Abdullahi Ganduje ya yi wa Gwamna Abba Yusuf na Kano, cewa ya zo ya shiga APC, ya zame masa abin zolaya daga bakin akasarin ‘yan Kwankwasiyya a Kano.
A ranar Laraba da dare Ganduje ya dira filin jirgin Malam Aminu Kano, a ziyarar sa ta farko tun bayan saukar sa daga mulki, bayan NNPP ta kayar da ɗan takarar APC, Nasiru Yusuf.
A taron APC da Ganduje ya jagoranta a Kano ranar Alhamis, ya yi kira ga Gwamna Abba da sauran ‘yan NNPP da ma sauran jam’iyyu cewa su shigo APC, jam’iyya mai mulki a sama.
Ganduje ya ce nan gaba Kano za ta koma jam’iyya ɗaya.
Kiran da Ganduje ya yi wa Abba ya zo ne a daidai lokacin da wasu ke yaɗa cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya nemi Ganduje ya je ya sasanta da tsohon ubangidan sa, Rabi’u Kwankwaso, madugun Kwankwasiyya.
Editan PREMIUM TIMES ya tambayi Kwankwaso yiwuwar shiryawa da Ganduje, ko kuma yiwuwar komawa APC, amma sai ya ce ba a ƙasar, kuma ya kashe waya.
A ɓangaren ‘yan Kwankwasiyya kuma, su na cike da mamakin yadda Ganduje ya zo Kano, maimakon ya yi kira a sasanta, sai ya nemi Gwamna ya shigo APC.
“Kai da aka kayar da ku zaɓe, har a Kotun Ƙoli, ai kai ne ya kamata a yi maka tayin shigowa jam’iyyar NNPP wadda ta kayar da ku, domin ku ke da matsala ba NNPP ba.” Cewar wani ɗan Kwankwasiyya.
Ganduje ya ce ya na ƙoƙarin ganin sun ƙara yawan magoya bayan APC a Kano, ta hanyar jawo ‘yan wasu jam’iyyu a cikin jam’iyyar.
Sai dai kuma da dama na ganin cewa ai Ganduje ba shi da baƙin da zai fito ya yi wa ɗan NNPP tayin shiga APC, jam’iyyar da suka ce a yanzu ba ta da farin jini a Kano, kuma sun kayar da jam’iyyar a lokacin da ma take da farin jinin ta.
Discussion about this post