Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin ministoci shida, waɗanda za su yi wa Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu (NSIP) garambawul.
Kafa kwamitin ya biyo bayan dakatar da shirin da Shugaba Tinubu ya yi, mako ɗaya bayan dakatar da Ministar Harkokin Agaji da Jinƙai, Betta Edu.
Tinubu ya dakatar da Edu, bayan sauke jagorar raba Tattalin Marasa Galihu, Halima Shehu.
An zargi dakatacciyar Minista Edu da karkatar da Naira miliyan 585.2 cikin asusun bankin ma’aikaciyar Gwamnatin Tarayya.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Asabar, ya ce kwamitin wanda Tinubu ya naɗa, ya ƙunshi ministoci shida ƙarƙashin Ministan Harkokin Kuɗaɗe, kuma Ministan Kula da Tattalin, Wale Edun.
Sauran sun haɗa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, Ministan Lafiya, Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu.
Sauran sun haɗa da Minsitan Sadarwa da Ƙaramin Ministan Harkokin Matasa.
Nauyin Da Aka Dora Wa Kwamitin:
“An ɗora wa Kwamitin Musamman na Shugaban Ƙasa nauyin gaggauta fara bin-diddigin kashe kuɗaɗen Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu da kuma duba tsare-tsare da ƙa’idojin shirin baki ɗaya.
“Za su yi haka ne domin sake wa shirin fasalin tsare-tsaren raba kuɗaɗe a ayyukan tallafin marasa galihu, shirin ciyar da ‘yan makaranta da tallafa wa masu ƙananan sana’o’i. Sai kuma Shirin N-Power da na tallafin kuɗaɗe ga marasa galihu,” cewar Ngelale.
Discussion about this post