Shugaba Bola Tinubu ya karya wata sabuwar doka da ya saka a kwanakin baya na rage yawan ƴan rakiya da za su rika tafiya tare da shi yayin balaguro na cikin gida da waje.
A ranar Talatar makon jiya shugaba Tinubu ya sanar da dokar da aka yi wa jami’an da ke raka shi da wasu manyan jami’an gwamnati a tafiye-tafiyen gwamnati.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya ce dokar hanya ce ta rage kuɗaɗen da ake kashe wa kawai don rage facaka da kuɗaɗen gwamnati.
Amma kasa da mako guda da sanar da sabuwar dokar da kuma fara aiki, shi kansa shugaba Tinubu ya karya ta. PREMIUM TIMES ta gano cewa a ranar Litinin ya ta fi jihar Imo domin halartar bikin rantsar da Gwamna Hope Uzodinma a karo na biyu kuma na karshe, da mutane sama da 50 cikin tawagarsa.
A tafiyar sa ta farko tun bayan aiyana sabuwar dokar, shugaba Tinubu ya tashi da akalla mutane 25 a cikin jirgin shugaban kasa zuwa Owerri, babban birnin jihar Imo. Akalla wasu jami’ai 30 ne suka isa jihar kafin isowarsa birnin.
Wasu daga cikin wadanda suka yi tafiyar tare da shugaban kasa a jirgin sa NAF 001, sun haɗa da dansa, Seyi Tinubu; babban mataimaki na musamman/ sakatare mai zaman kansa, Aderemi Damilotun; babban sakataren sa, Hakeem Muri-Okunola; babban mataimakinsa na musamman kan harkokin gida; Subair Oluwatoyin da babban mataimaki na musamman kan harkokin zamantakewa, Atika Ajaka.
Baya ga waɗannan ƴan rakiya da suka yi tafiya da Tinubu, akwai wasu mutum 30 da suka bi jirgin kasuwa suka yi gaba kafin isowar Tinubu Imo.
Cikin tawagar da suka yi gaba akwai mai taimaka wa Tinubu kan harkar ƴaɗa labarai, AbdulAziz AbdulAziz da wasu maƙarraban sashen watsa labarai na ofishin shugaban kasa.
Sannan kuma akwai jami’an tsaro da aka tafi da su masu yawa don kawai rakiya.
Discussion about this post