Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya sha alwashin cewa a karkashin mulkin sa zai rangaɗa ayyukan ci gaba a ƙauyuka da kananan hukumomin jihar Kaduna.
Da ya ke hira da Talbijin ɗin Arise, gwamna Sani ya ce baya ga ayyukan ci gaba, ya lashi takobin haɗa kan mutanen jihar Kaduna gaba ɗayan su.
” A jihar Kaduna, burin mu shine mu haɗa kan mutanen jihar, ba tare da nuna banbanci na addini ko ƙabila ba.
” Idan ba a manta ba a taron kaddamar da wasu ayyuka da muka yi a ƙaramar hukumar Zangon Kataf, Zamani Lekwot da kansa ya yaba wa ayyukan da muka bijiro da su domin ci gaban mazauna kananan hukumomin mu, musamman mazauna ƙarkara
Daga nan sai gwamna Sani ya ce, abin da ya faru a gwamnatin baya, sun wuce, yanzu sabon faifai aka saka.
” Dole ne mu maida hankali wajen kai ababen more rayuwa kananan hukumomin mu domin mutanen mu na karkara. Da haka ne kowa zai shaida ayyukan gwamnati.
Discussion about this post