Daren jiya an sha ruguntsimin amon ƙarar tashin ‘yar rototuwar da yara da matasa ke bugawa domin murnar shigowa sabuwar shekara ta 2024.
An shiga sabuwar shekarar cike kyakkyawan fatan cika alƙawurran da aka ɗaukar wa ‘yan Najeriya na samar masu mafita daga halin ƙuncin da suka afka, da kuma wanda aka tunkuɗa su a ciki, suka rufta ba shiri.
Shekaru shidan ƙarshen 2023 sun kasance a wurin talakawa wani dogon zangon rayuwa cikin ƙuncin raɗaɗin tsadar rayuwa dalilin cire tallafin fetur da aka yi da kuma sakin Naira a kasuwa domin ta ƙwatar wa kan ta daraja.
Haka nan kuma ƙarshen 2023 ya kasance bala’i ta wasu da dama da suka rasa rayukan su da ma waɗanda suka jikkata.
To, abin lura dai shi ne duk irin yadda masu sukar Shugaba Bola Tinubu za su matsa ƙaimi, to sun dai san cewa sun gaji tattalin arzikin ƙasa a hannun tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda babu komai a jikin sa, tamkar aholakin jaki, maimakon a gaji tattalin arzikin ƙasa mai kitse kamar bajimin sa.
Tinubu ya gaji baitilmalin da babu komai a cikin ta. Ya gaji gagarimin cin hanci da rashawa da mahaukaciyar satar kuɗaɗe daga gwamnatin Buhari, da kuma sauran matsaloli daban-daban.
Amma duk da haka, sai Tinubu ya kama sitiyarin motar Najeriya, ya ɗau hanya, ya darzaza. Bai damu ba, domin dama ya ce kada a tausaya masa ganin irin gagarimar matsalolin da ya gada. Ya ce tun farko ya san zai iya fuskantar ƙalubalen dukkan su, shi ya sa ya ce a zaɓe shi zai iya.
A gaskiya ta fuskoki da dama dai Tinubu ya nuna cewa a shirye ya ke ya kawo canjin da ake buƙata, sai dai kuma ba abu ba ne da za a samu a sauƙaƙe, kuma ba abu ne da za a yi saurin gani ba a farat ɗaya.
Amma abu mafi kyau a ɓangaren sa shi ne irin yadda ya nuna cewa shirye ya ke ya samar da canjin da ake buƙata.
Shugaba Tinubu ya shata wa Ministoci mizani ko ma’aunin da za su cika maƙil da ayyukan ci gaba, kuma ya yi bazaranar cewa duk wanda ya kasa cika ma’aunin sa, to zai maida shi ƙauyen su kawai.
Tinubu ya naɗa Hadiza Bala Usman Mataimakiyar Musamman kan Tsare-tsare domin ta jagoranci Sashen Auna Mizanin Ayyukan Ministoci.
A taron sanin makamar aiki da aka shirya wa sabbin ministoci da manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya ta hadiman shugaban ƙasa da manyan Sakatarorin Gwamnatin Najeriya. A wurin taron dai Tinubu ya bugi ƙirji ya ce, “Tilas sai na yi nasara, ko ta halin ƙaƙa.”
“Ku kuma Ministoci na, duk wanda ya yi aiki tuƙuru to ba shi da wani haufi ko tsoro, amma wanda muka auna ayyukan sa muka ga bai taɓuka komai ba, za mu tsige shi mu tura shi gida. Babu wani ɗan mowa ko ɗan bowa a wuri na. Duk ɗaya ku ke, babu wani shafaffe da mai.” Gargaɗin da Tinubu ya yi wa ministocin sa kenan.
Irin yadda Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya ɗauki umarnin Shugaba TInubu da muhimmanci ya sa kowane Ministan Tinubu ya shiga taitayin sa. Domin kwana biyu bayan gargaɗin Tinubu, Keyamo ya kori manyan daraktocin ma’aikatar su shida. Bayan ya kore su, Keyamo ya shaida wa manema labarai cewa, “ba zan yarda wani ya goga min laifin da za a kore ni ba. Da a kore ni, gara na kori wanda zai yi min silar a kore ni.”
Maganar gaskiya akwai jan aiki a gaban Shugaba Tinubu. Saboda har yanzu dai matsalar tsaro kamar ma ba a fara tunkarar ta ba, idan aka yi la’akari da kashe-kashen da ke faruwa a yankuna daban-daban. Kisan gillar da aka yi a ƙananan hukumomin Ɓakkos da Barikin Ladi a Jihar Filato a ranar Jajibirin Kirsimeti, sun kasance mummunan babin da ƙarshe a bala’o’in shekarar 2023. An kashe sama da mutum 150, kuma saboda wannan gagarimar matsala ce Shugaba Tinubu ya ware wa matsalar tsaro har Naira tiriliyan 3.25 a kasafin 2023.
Sannan kuma an umarci a cire ‘yan sanda daga wurin manya da masu hannu da shuni, a maida su wajen ayyukan samar da tsaro. Saboda haka tilas a bi wannan umarnin, domin a samu biyan buƙatar daƙile matsalar tsaro.
Akwai matsaloli da yawa, kuma Shugaba Tinubu da muƙarraban sa kamar irin su EFCC da binciken Babban Bankin Najeriya, CBN duk sun nuna abin fa da gaske ake yi.
Fatan mu shi ne yadda aka fara warware wannan zaren, to a tabbatar da an kai ƙarshen saƙa, ba tare da an yi sakacin da zaren ya kuɓuce ko ya suɓuce ko ya tsinke ya koma cikin kwarkwaron sa ba.
Discussion about this post