Ɗaukacin Musulman Jihar Ondo sun yi wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ƙorafin cewa ya fifita Kiristoci, sannan ya maida Musulman jihar saniyar-ware wajen rabon muƙaman gwamnati.
Sun yi wannan ƙorafin ne yayin ziyarar da suka kai masa a ranar Talata, a Gidan Gwamnatin Ondo.
Tawagar da ta kai masa ziyarar dai ta na ƙarƙashin jagorancin Shugaban Limamai da Alfa-Alfa na Jihar Ondo, Ahmed Aladesawe.
Da ya ke wa Gwamna jawabi, Aladesawe ya yi kira da tsokaci gare shi da gyara rashin adalcin da ya yi wajen rabon muƙamai, ta hanyar sanya Musulmai cikin gwamnatin sa.
Ya ce zai yi amfani da damar ziyarar domin miƙa ta’aziyyar Musulman jihar dangane da rasuwar tsohon Gwamna Rotimi Akeredolu, kuma su taya Aiyedatiwa murnar hawa kujerar gwamna da ya yi.
“Sai dai kuma muna nuna rashin jin daɗin ganin yadda dukkan muƙaman da ka raba tun bayan hawan ka mulki, ba su yi daidai da mizanin adalci ga ɗaukacin Musulmai na jihar nan ba.
“Gwamnatocin baya sun ware musulman jihar Ondo, an maida mu kamar ba mutane ba. Mu ba a sa mu cikin gwamnati ba, kuma mu gwamnati ba ta ja mu a jika ba.
“A zamanin gwamnatin marigayi Akeredolu, babu Musulmi ko ɗaya a manyan muƙamai 10 na Gwamnatin Jihar Ondo, wato kama daga Gwamna, Mataimakin Gwamna, Sakataren Gwamnatin Jiha, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Babban Sakataren Yaɗa , Kwamishinan Shari’a, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jiha, Kakakin Majalisar Jiha, Mataimakin Kakakin Majalisar Jiha da kuma shugaban jam’iyya.” Inji shi.
Ya ce duk ƙoƙarin da su ka riƙa yi domin tsohon gwamna ya gyara wannan rashin adalci, bai shiga kunnen sa ba har ya mutu.
Haka kuma jagoran tawagar Musulmai ya ce wa Gwamna Aiyedatiwa ba su ji daɗin yadda ya yi manyan naɗe-naɗe har huɗu tun bayan yawan sa mulki, amma bai naɗa Musulmi ko ɗaya ba.
“Ko ka na tunanin babu wani Musulmin da ya cancanta ne? Ko ka na nufin babu haziƙai, ƙawararru kuma masu ilmin da suka cancanta daga cikin Musulmi?”
Yayin da Gwamna ya ce dukkan naɗe-naɗe huɗu da ya yi duk bisa cancanta ne ya yi su, ya sha alwashin ci gaba da goyon bayan Musulmin jihar a dukkan ɓangarorin da suka kai koken su.
Discussion about this post