‘Yan bindiga sun bindige Haruna Abale, dagacin Kukar Babangida, garin da ke ƙarƙashin Ƙaramar Jibiya a Jihar Katsina.
Kisan wanda ya faru da jijjifin safiyar Alhamis, ya ritsa da wasu mutum 9, ciki har da ɗan sa Idris Haruna.
Majiya da dama sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigar sun fara dira gidan dagacin, inda suka bindige shi da ɗan sa, da kuma wasu mutum huɗu.
Sannan kuma sun banka wa gidaje da motoci da kantina wuta a garin.
“Ina tabbatar maka cewa wannan harin sun zo ne gadan-gadan don su kashe basaraken garin, wanda ya tsananta sosai wajen fitowa ya na magana mai kaifi ga ‘yan bindiga,” haka wani jigo a ƙauyen Babangida ya shaida wa wakilin mu.
“Saboda gidan sa suka fara dira kan su tsaye, inda wasu ‘yan bindigar suka kewaye gidan sa, wasu kuma suka afka cikin gidan.”
Maharan sun shiga garin wajen ƙarfe 1 na dare, kuma suka shafe sa’o’i da dama kafin su fita.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan mamacin wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce ɗan uwan sa Idris da aka bindige da sauran mutum huɗu ɗin, su na kwance ne inda ‘yan bindigar su ka kulle su cikin wani ɗaki, daga nan suka buɗe masu wuta.
“Abin fa ya yi muni ƙwarai. Sun afka cikin ɗakin mahaifi na, suka yi ta harbin sa ba sau ɗaya ko sau biyu ba. Daga nan suka tafi ɗakin ɗan uwa na Idris suka harbe shi da abokan sa huɗu waɗanda ke kwana a gidan,”
PREMIUM TIMES ta samu cikakken bayanin cewa a lokacin da wasu ‘yan bindigar ke cikin gidan basaraken, wasu kuma sun shiga cikin garin suka riƙa yin harbin kan-mai-tsautsayi.
“Sun kashe mutum huɗu waɗanda suka fito daga cikin gidajen su da niyyar gudun tsira, saboda tsananin rugugin ƙarar bindigogi.”
Shugaban Ƙaramar Hukumar Jibiya, Bishir Sabi’u ya tabbatar da afkuwar mummunan lamarin a zantawar sa da manema labarai.
Haka ita ma Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Kakakin ta Abubakar Sadik ya tabbatar da kai harin.
Ya ce baya ga kisan mutum 9, sun kuma ƙone motoci biyar.
Discussion about this post