Tashin farashin kayan abinci ya yi ƙololuwar da ta kai shi har kashi 28.92 cikin 2023. Wannan lamari ya haddasa tsadar rayuwar da ta galabaita miliyoyin ‘yan Najeriya a ahekarar, har ta kai gidaje da dama ba a iya ɗora girki sau uku a rana kamar yadda ɗan Adam ya ke yi a rayuwar sa.
Cikin watan Nuwamban 2023 tsadar ta kai kashi 28.20, amma zuwa Disamba sai da malejin ya dangwale har kashi 28.92.
Wannan ƙididdiga dai ta fito daga Ofishin Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai na Ƙasa (NBS), wanda mallakar Gwamnatin Tarayya ne.
Ƙididdigar wadda aka fitar ranar Litinin, ta nuna cewa tsadar kayan abinci ta ƙaru da 0.72 tsakanin Nuwamba zuwa Disamba 2023.
NBS ta ce amma idan aka auna tsadar rayuwar 2022 da ta 2023, to za a ga cewa a Disamba 2022 malejin ya na kashi 21.34 ne, amma kuma a Disamba 2023, ya dangwale kashi 28.92.
Farashin abinci ya dangana 33.93 a Disamba 2023 idan aka kwatanta da farashin Disamba 2022 lokacin da ya ke kashi 23.75.
Watannin tsakiyar 2023 ne kayan masarufi da na sauran nau’ukan kayan da ake sarrafawa cikin gida suka yi tashin-gwauron-zabo, saboda cire tallafin fetur da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi, a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Lamarin ya sa tsadar fetur ta buwayi kowace sana’a ko aiki a faɗin ƙasar nan. Bincike ya nuna cewa gidaje da dama ana fashin daga abinci sau uku a rana. Wasu kuma ana fashin dafawar ma ɗungurugum a wata ranar.
Discussion about this post