Shugaban karamar hukumar Ikwerre Samuel Nwanosike wanda ɗan gani kashe nin tsohon gwamna Nyesome Wike ya gurza wa gwamnan Ribas Simi Fubara rashin mutunci da ba shi misaltuwa, inda ya bayyana a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan yanar gizo cewa gwamnan sultune, butulu kuma Shashasha.
A bidiyon Nwanosike ya ce, ” Babu abin da ka taɓuka tun da ka zama gwamna sai lafta wa wasu kuɗaɗe su rika zagin tsohon gwamna Wike.
” Ko wani gwamna ya na aiki, sannan, mutanen sa sun fara shaida sabuwar gwamnati a jihohin su amma kana can kana kama tasha, ka tasa tsohon gwamna a gaba a faɗan da ba za ka iya ba.
Ya kamata Fubara ya gaya mana irin ayyukan da ya yi zuwa yanzu baya ga daukar kudinmu da kuma bayar da cin hanci don cin mutuncin Wike,”
Ya zargi Gwamna Fubara da daukar nauyin rashin tsaro a Abuja domin Shugaba Bola Tinubu ya tsige Wike daga mukamin ministan Abuja.
“Ya Riƙa tura mutane Abuja suna gulman cewa Wike koma Ribas yana siyasa (yayin da a Abuja) ana ta fama da yin garkuwa da mutane. Hakan na nufin Fubara na cikin wadanda ke goyon bayan sace mutane a Abuja saboda yana son a ga gazawar Wike, Tinubu ya kore sa.
” Ina so ya sani cewa Tinubu ya san ko wanene Wike, saboda haka tuggun da yake ƙulla masa ba za su yi tasiri ba. Domin ko a tarihin jihar Ribas, ba bu wanda ya taɓa yin aikin da Wike ya yi wa mutanen jihar.
Discussion about this post