Mai horas da ƴan wasan Super Eagles Jose Peseiro ya bayyana cewa Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Super Eagles da Guinea-Bissau.
Peseiro ya ce ba Yusuf ba akwai yiwuwar shima Zaidu Sanusi da Troost Ekong ba za su buga wasan ba.
Yayin da yake jawabi da manema labarai a Abidjan ranar Litinin, Peseiro ya ce har yanzu Yusuf bai warke ba, sannan shi ma Zaidu da Ekong duk suna da matsala a kafafun su.
” Dalilin da ya sa ke nan na ce suma mutum biyu da Ekong da Zaidu kila ba za su buga wasa ba. Muna duba ƴan wasan mu, kada mu takura musu yayin da muna sa ran akwai muhimman wasanni a gaban mu.
” Ba mu hangen nesa yanzu, kowanne wasa muna binta ne yadda ta zo mana, mu doka ta yadda ba za a raina mu ba, sannan mu kuma nuna wa sauran kasashe cewa da gaske muke yi.
Saboda haka ba za mu raina Guinea-Bissau ba, su mama za mu fito musu ba da wasa ba.
An hango Yusuf, Zaidu da Ekong suna atisayin su a gefe da ban.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda likitocin Najeriya, suka bada rahoton gulɗewar Sadiq Umar, wanda bayan ya koma kungiyarsa ta Real, likitocin can suka ce kuje yayi kawai.
Tuni har ya fara buga tamola a can Spain.
Discussion about this post