Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Tarayya (FIRS), ta bayyana cewa ta tara har Naira tiriliyan 12.374 a matsayin haraji cikin shekarar 2023.
Wannan adadi dai ya zarce adadin da aka nemi tarawa tun da farko a shekarar, wato Naira tiriliyan 10.7.
Shugaban Hukumar FIRS, Zacch Adedeji ne ya bayyana haka a wani taron da FIRS ta shirya na sanin-makamar-aiki na kwana biyu, a Ɗakin Taron Transcorp Hilton, Abuja.
Taron wanda aka buɗe a ranar Laraba, ya ce Gwamnatin Tarayya ta bai wa FIRS umarnin ta yi dukkan ƙoƙarin da za ta yi domin ganin ta tara haraji na aƙalla Naira tiriliyan 19.4 cikin shekarar nan ta 2024.
Adedeji ya ce FIRS za ta cimma wannan ƙudiri na ganin ta tara Naira tiriliyan 19.4 a 2024 ɗin, tare da yin amfani da kyakkyawan tsarin karɓa da tara kuɗaɗen haraji, tare kuma da samar da dama da masu masana’antu za su yi harkokin su.
A wurin taron, Ministan Harkokin Kuɗaɗe Wale Edun ya jinjina wa Adedeji ganin ya zarce adadin da aka umarce shi ya tara a 2023.
Wata babbar jami’ar FIRS mai suna Amina Ado, ta ce an tara Naira tiriliyan 3.17 daga harajin harkokin fetur, harkokin da ba na fetur ba kuwa an tara Naira tiriliyan 9.2.
Tun da farko dai Naira biliyan 10.7 aka nemi FIRS ta tara.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban FIRS, Dare Adekanmbi.
Discussion about this post