‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da mutum 31 a ƙauyen Tashar Nagulle da ke Ƙaramar Hukumar Batsari, sun nemi a biya su diyyar Naira miliyan 60 kafin su sake su.
Wani mazaunin ƙauyen ya tabbatar wa PREMIUM TIMES wannan mummunan labari.
Maharan sun kai farmaki a ƙauyen ranar Lahadi, inda suka yi awon-gaba da mutum 31, kamar yadda PREMIUM TIMES ta wallafa washegarin kai farmakin.
Sun yi amfani da lambar wayar ɗaya daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su, inda suka kira iyalan sa, suka ce su na so su yi magana da dagacin ƙauyen.
“Mu talakawa ne, ba mu da halin haɗa Naira 60,000 ma ballantana kuma har Naira miliyan 60,” haka wani hadimin dagacin ƙauyen ya shaida wa wakilin mu. Ya ce a gaban sa ‘yan bindigar suka kira dagacin suka nemi waɗannan maƙudan kuɗaɗe.
“Ai rashin tunani ne ma a nemi Naira miliyan 60 a hannun mu. Ina muka gan ta? Muna roƙon hukuma ta fito ta kawo mana ɗauki, saboda al’amurra sun dagule mana. Ko gonakin mu ba mai iya zuwa. Kuma ba mu iya fita cin kasuwannin ƙauyuka.”
“Ran maharan ya ɓaci da suka ji ba mu iya haɗa masu Naira miliyan 60. Jiya sun bugo waya sun nemi mu kai masu niƙaƙƙen buhun garin turo, kuma mu kai masu jarkoki biyu domin su riƙa zuba ruwan sha. Sannan mu haɗa masu da kayan miya.” Inji wani malami da ke ƙauyen, wanda ya nemi mu sakaya sunan sa.
Ya ce mutanen ƙauyen sun fara tara ɗan abin da Allah ya hore masu, domin su kai wa ‘yan bindigar.
“Mun fara tattara ɗan abin da ya sauƙaƙa, domin ‘ya’yan mu da abokan mu da matan mu da dangin mu aka kama. Ba za mu iya barin su cikin daji a hannun ‘yan bindiga ba.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Mahara suka kutsa Tashar Nagulle suka gudu da mutum 31, a yankin Batsari.
Gungun ‘yan bindiga fiye da su 100 sun shiga ƙauyen Tashar Nagulle, suka tattara mutane wuri ɗaya, sannan suka darzaza cikin daji da mutum 31.
Wannan mummunan lamari ya faru ranar Lahadi da dare kafin 9 na dare.
Tashar Nagulle na cikin Ƙaramar Hukumar Batsari, yankin da kwanan baya ‘yan bindiga suka afka wa sansanin sojojin da ke kusa da garin.
Waɗanda aka yi garkuwa da su dai sun haɗa da mata, ƙananan yara da kuma magidanta.
Wakilin mu ya tattauna da mutum biyu ‘yan ƙauyen Tashar Nagulle, kuma dukkan su sun nemi a sakaya sunayen su.
Wani malamin addinin Muslunci ya ce maharan sun kewaye ƙauyen, kuma su na sanye da kayan sojoji yawancin su.
Ya ce dukkan su a ƙasa suka yi tattaki zuwa cikin garin, saboda sun ajiye baburan su can nesa.
“Ai ni dai ina zaune ƙofar gida tare da wasu abikai na, wajen 9 na dare, sai muka ji tashin ƙarar bindigogi.
“Muka yi sararaf za mu fece a guje, amma sai ‘yan bindigar suka ce mana kada mu gudu, wai su jami’an tsaro ne aka aiko su kare mu.” Haka malamin ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho.
Ya ce maharan “sun san idan suka ce su sojoji ko ‘yan sanda ne aka turo za su kare mu, to wannan yarda za mu yi. Kuma abin da ya faru kenan,” inji shi.
Majiya ta ce daga nan sai mutanen gari suka fara taruwa tsakiyar garin, ba tare da sun san cewa masu garkuwa da mutane ba ne. Saboda wasun su na sanye da kayan sojoji.
Wani magidanci kuwa shaida wa wakilin mu ya yi cewa ai shi da dai ya fece a guje bai tsaya ba. Duk kuwa da cewa sun ce jami’an tsaro ne, amma shi dai zuciyar sa ta ce ka arce kawai.
“Na gudu na shige ƙarƙashin gadon mata ta na ɓoye. Saboda idan irin haka ta taso, har gara mutum ya ɓoye ƙarƙashin gado, maimakon ka shiga daji a guje. Saboda za ka iya haɗuwa da su a daji idan wasu sun rarrabu,” inji shi.
Malamin nan kuwa cewa ya yi bayan maharan sun kewaye su, sai suka ce mu biyo su. To daga nan muka gane cewa mun faɗa hannun mugayen.”
Ya ce ana cikin tafiya ya riƙa tsayawa baya-baya, har ya sulale ya koma cikin gida ya ɓoye.
“Zuwa yau Litinin dai mun nemi mutum 31, ba mu gani ba. Kuma duk an shiga daji da su.” Inji shi.
Ya ce DPO na Batsari da ‘yan bijilante sun je garin, amma lokacin tuni aikin Gama ya gama.
Wakilin mu ya kira lambar wayar Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Abubakar Sadik-Aliyu, amma bai same shi ba. An yi masa saƙon tes, shi ma bai maida amsa ba.
Discussion about this post