Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da bunƙasa duk da matsalolin da ta ke fuskanta.
A cikin wata sanarwa ga manema labarai da ya bayar a Abuja a ranar Lahadi, ministan ya ce, “Ba za a ce ba a cikin wani yanayi na matsala da mu ka samu kan mu a ciki ba a matsayin mu na ƙasa: akwai hauhawar farashi da ya shafi kasafin kuɗin kashewar mutum da na gudanar da harkokin gida, da kuma barazana ga halin tsaro a wasu sassa na ƙasar nan.
“Amma duk wannan wani ɓangare ne na abin da ke faruwa. Su ma matakan da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ke namijin ƙoƙarin ɗauka a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin magance waɗannan matsalolin, abin dubawa ne.
“Mu na da cikakkiyar masaniyar haƙƙin kulawa da ya rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya ga kowane ɗan Nijeriya ba tare da la’akari da shekaru, jinsi, addini, ƙabila ko matsayin sa a al’umma ba.
“A ɓangaren tsaro, ana tunkarar duk wata barazana. Mu na kai hari kai-tsaye ga sansanonin ɓarayi, tare da cimma kyawawan nasarori. A makon jiya, an kashe ko an kama ɗimbin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda.
“Rikicin da ya sake kunno kai a Jihar Filato, a gaskiya abin baƙin ciki ne, amma mu na tabbatar wa da kowa da kowa cewa ana gurfanar da duk masu jawo fitina a can da ma sauran sassan ƙasar nan a kotu. Za a yi masu shari’a, kuma za a dawo da zaman lafiya a dukkan wuraren da abin ya shafa.
“Mu na yaba wa namijin ƙoƙarin da hukumomin tsaro da masu farin kaya ke yi, waɗanda ba su yi sanyi a gwiwa ba don tabbatar da cewa mun samu natsuwa a gidajen mu da kan titunan mu, sannan masu aikata laifi ba su samu sauƙi ba.
“Dangane da tattalin arziki, dukkan ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya da abin ya shafa su na aiki tare da juna domin su rage tashin farashi, su daidaita tsarin canjin kuɗin ƙasar waje, kuma su samar da yanayi mai kyau don haɓaka harkar kasuwanci da zuba jari. Irin Nijeriyar da Shugaba Tinubu ya ke ƙoƙarin ginawa ita ce wadda ba a bar kowa a baya ba.
“Ana ta fito da tsare-tsare masu tasiri, waɗanda su ka haɗa da Shirin Bada Rance Ga Ɗalibai, shirin Shugaban Ƙasa na samar da motocin haya na CNG masu aiki da lantarki domin rage dogaro da fetur da man dizel, da sauran tsare-tsaren bada lamuni domin kasuwanci. Shirin samar da motocin zai rage tsadar kuɗin shiga motar haya da sama da kashi 50 cikin ɗari.
“Mu na kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da waɗannan damarmakin da zarar an fito da su, domin an yi su ne saboda kowa ya amfana.
“A daidai lokacin da mu ke tunkarar matsalolin mu haiƙan, ya kamata mu tuna wa dukkan ‘yan Nijeriya da su guji sauraren duk wasu muggan labarai da kalamai na ƙarya da ke jawo rarrabuwar kai. Misali, ba gaskiya ba ne cewar za a mayar da hedikwatar Hukumar Tashoshin Jiragen Sama ta Tarayya ta Nijeriya (FAAN) da wasu sassan Babban Bankin Nijeriya (CBN) zuwa Legas saboda dalilai na siyasa domin a ware wani sashe na ƙasar nan. Waɗannan zarge-zargen ba su da wata makama. Maimakon haka, waɗannan matakai ne da su ka shafi gudanarwa domin a inganta harkar aiki da rage kashe kuɗi.
“Ina kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su kula da duk wasu mutane da ƙungiyoyi a gida da ƙasar waje waɗanda su ka ƙware wajen yaɗa labaran bogi a gidajen rediyo da talabijin da soshiyal midiya, sannan su na yaɗa guntayen bidiyo da hotuna da aka sauya wa fasali don sakawa a intanet.
“Tilas mu zama tsintsiya-maɗaurin-ki-ɗaya kan waɗannan waɗanda ke ta neman su ga sun farraƙa mu. Nijeriya tamu ce mu duka, kuma aikin gina irin Nijeriyar da mu ke mafarkin samu namu ne gaba ɗayan mu, ba tare da la’akari da addinin mu ko ƙabilar mu ko inda mu ka fito ba. Saboda haka ne mu ka fito da Ƙudirin Saka Ɗa’a a Zukatan ‘Yan Nijeriya, wato ‘Nigerian National Values Charter’ (NVC), wanda wani daftari ne na yarjejeniya tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa, a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin dawo da fata tagari, amintaka da haɗin kan ‘yan ƙasa.
“A matsayin wani ɓangare na samar da amintaka a tsakanin ‘yan Nijeriya, za a ci gaba da yaƙin nan kan cin hanci da rashawa, kuma za a zurfafa shi. Don tabbatar da cewa babu wani ɗan lele, kuma an yi amfani da dukiyar jama’a wajen yi wa jama’a aiki, Shugaba Tinubu ya na sama wa hukumomin yaƙi da cin hanci dukkan goyon bayan da su ke buƙata domin gudanar da aikin su.
“Ba za mu cimma nasarar gina irin Nijeriyar da mu ke so ba idan har mu ka kafe kan kallon ƙalubalen mu da matsalolin mu kaɗai, ba ɗimbin damarmaki da kyawawan labarai da ke zagaye da mu ba. A sane mu ke cewa ƙasar na ci gaba da samun burin zuba jari daga ‘yan kasuwa na gida da na waje.
“A cikin makwannin farko na buɗe kasuwar hannun jari ta 2024, har Kasuwar ta sa ana maganar mu a duniya saboda kyakkyawar ribar da ake samu a cikin ta. ‘Yan kasuwar Indiya da su ka yi alƙawarin zuba sabon jari dala biliyan 14 a Nijeriya a lokacin Taron Ƙoli na G20 da aka yi a ƙasar Indiya cikin Satumba 2023 har sun fara cika wannan alƙawarin nasu. A sassan hadahadar fetur da iskar gas da aikin gona, kayan masarufi, makamashin da ake juyawa, kiwon lafiya, sadarwar zamani, da sauran su da dama, mu na ganin kamfanonin cikin ƙasa da na waje su na bayyana amannar su kan damarmaki marasa iyaka da ke jibge a Nijeriya.
“Nasarori masu sanyaya rai da ƙungiyar mu ta ƙwallon ƙafa ta Super Eagles ta ke samu a gasar Cin Kofin Ƙasashen Afrika da ke gudana yanzu a Kwat Debuwa wasu misalai ne abin lura; tuni ne da ya zo kan kari wanda ke alamta cewa abubuwan da ke riƙe da mu sun fi abubuwan da su ka raba mu ƙarfi.
“Kada mu manta da ainihin abin da yake dahir: wato maimakon rarrabuwar kai da gaba da juna, za mu iya zama tare kuma mu bunƙasa cikin haɗin kai da fata tagari, tare da tabbacin cewa duk da waɗannan matsalolin masu wucewa da koma-baya da ake samu daga lokaci zuwa lokaci, babbar nasara ta na gab da zuwa.”
Discussion about this post