Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana rashin jin dadinsa kan gine-ginen da aka fara yi a Jami’ar Fasaha ta Abuja dake gundunmar Abaji.
Wike ya fadi haka ne a taron da ya yi ranar Juma’a da masu ruwa da tsaki na garin Abaji, yayin da ya ce Jami’ar ba ta sauya makarantar sakandare ba da hakan a cewar sa bai dace da martabar Babban Birnin Tarayyar kasar nan ba.
Da yake mayar da martani ga roko na kammala jami’ar a watan Satumba da shugaban karamar hukumar Abaji Abubakar Abdullahi ya yi Wike ya ce tsarin da aka gina a makarantar bai kai matsayin da ake bukata ba da hakan ya sa ba za a iya bude jami’ar a watan Satumbar bana ba.
Yayin da yake tabbatar wa mazauna garin Bwari da babban birnin tarayya Abuja aniyarsa na kammala jami’ar, ministan ya ce zai tattauna da sakatariyar ilimi domin yin nazari kan tsaron ginin jami’ar.
“Daga nan ne za ku ga irin rawan da za mu taka domin ganin an samar da kayan aiki masu inganci da nagarta domin jami’ar ta fara aiki yadda ya kamata.
Discussion about this post