Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru ya bayyana cewa irin muhimman ayyukan raya jiha da Gwamna Umar Namadi na jihar ke bijiro da su, hakan na tabbatar da cewa amincewar da ya yi a zaɓi Namadi a matsayin gwamnan da zai maye gurbin sa a jihar, ba zaɓen-tumun-dare ba ne.
Badaru wanda a yanzu shi ne Ministan Tsaro, ya kai ziyarar Jigawa a ranar Asabar, wadda wannan ita ce ziyarar sa ta farko tun da ya kammala wa’adin mulkin sa a ƙarshen Mayu, 2023.
Badaru ya je a matsayin babban baƙo na musamman, wanda ya aza harsashen gina rukunin gidajen da Gwamnatin Umar Namadi za ta gina guda 1,500.
An aza harsashen ginin a Panisau, wani yanki na Dutse, babban birnin jihar.
“Na yi farin ciki sosai da irin gagarimin ci gaba da na ga an samu. Na ga ɗimbin jama’a cike da farin ciki, kowa na fara’a. Ana ta faɗa min cewa na bar masu gadon ƙasaitaccen shugaba kuma jagora nagari, wanda duk takun da ya ke yi, ya na tafiya ne tare da ayyukan cika alƙawurran da ya ɗauka.
“Ai na shaida maku tun a lokacin kamfen kafin zaɓe cewa mai gaskiya ne, kaifi ɗaya ɗaya ne, mutum ne da ba ya yin baki-biyu, kuma mai kuzari ne.
“Allah ya nuna maku cewa zaɓin da na yi na nuna cewa Umar Namadi za a zaɓa domin ya gaje ni, ba zaɓen-tumun-dare ba ne.
“Irin muhimman ayyukan raya karkara da inganta rayuwar jama’a da gwamnatin sa ke yi, na tabbatar zai yi fiye ma da abin da na aikata.
“Na gode ƙwarai da ku ka ba mu amana, mun bar jihar a hannun jagora kuma shugaba nagari wanda zai ci gaba da yin dukkan ayyukan da suka dace,” inji Badaru, lokacin da ya ke aza harsashen ginin gidajen.
Gidajen dai za su ƙunshi guda 1,500 ne za a gina a faɗin jihar, inda a Dutse babban birnin jihar za a gina guda 600.
Gwamna Umar Namadi ya ce gwamnatin Jihar Jigawa ce da kan ta za ta ɗauki nauyin gina gidajen baki ɗaya.
Ya ce za a gina gidajen a dukkan masarautun jihar guda biyar a hedikwatocin su, da kuma wasu garuruwa uku.
Wato kenan za a gina gidajen a Dutse, Ringim, Hadejia, Gumel, Kazaure da Kafin Hausa, Birnin Kudu da kuma Ɓaɓura.
Badaru ya ce za a ƙara gina wasu gidajen da zarar jama’a sun shiga cikin waɗannan da za a fara ginawa a garuruwan takwas.
Ya ce gina gidajen na ɗaya daga cikin alƙawurran sa a lokacin kamfen.
Namadi ya ce aikin ginin zai samar wa ɗimbin matasa da magidanta ayyukan wucin-gadi a lokacin da ake aikin ginin da ma na dindindin bayan kammala ginin.
Discussion about this post