Ƴan ta’adda sun kashe wasu ‘yan kasuwa 8 da ke dawowa daga kasuwar mako-mako ta Jibia a kusa da kauyen Kukar Babangida da ke Jihar Katsina a ranar Lahadi.
An kashe ƴan kasuwan ne a lokacin da ‘yan ta’addan suka bude wuta kan motar da suke ciki, inda suka yi awon gaba da wasu guda biyu yayin da maharan suka jikkata wasu fasinjoji hudu.
Wadanda suka jikkata, Bilyaminu, Malam Jafaru, Lawal Dadi da Dan Husuma, suna jinya a wani asibiti da ke yankin, kamar yadda wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho.
Wadanda aka kashe sun hada da Sani Na Gogara, Yusuf Karamin su, Sale Lami, Dan Hameme, Malam Shafi’i, Malam Dikke da Bashir Sani. Yayin da wadanda aka sace su ne Alhaji Abdurrashid da Abdu Teacher.
Wani jami’in tsaro a jihar Katsina wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa akwai yiwuwar ‘yan ta’addan na tserewa ne daga farmakin da sojoji suka kai a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadik, ya tabbatar da harin da aka kai wa ‘yan kasuwar, ya kuma ce rundunar ta dauki matakin hana afkuwar lamarin.
Discussion about this post