Gwamnan Kaduna Uba Sani ya umarci hukumomin tsaro da na gwamnati da du gudanar da bincike game da kisan dandazon ƴan maulidi da a sojojin saman Najeriya suka yi kuskuren ɗirka musu bamabamai.
Sojojin Saman Najeriya sun yi wa wasu mutane musulmi masu taron bikin maulidi a Tudun Biri, dake ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.
Sojojin sama cikin kuskure sun yi wa mutane ruwan bamabamai daga sama tunanin su ƴan bindiga ne.
Rahotanni sun kiyasta yawan mutanen da aka rasa ya kai mutum sama da 100.
Gwamna Sani ya yi alhinin wannan rashi da aka yi sannan ya ce za a gudanar da bincike domin tabbatar da abin da ya auku, sannan kuma tabbatar da irin haka bai sake aukuwa ba
Bayan haka gwamna Sani ya umarci da a garzaya da wadanda suka ji rauni asibitin Barau Dikko domin a duba su a kuma ba su magani.
“Na ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin. Mun kuduri aniyar hana sake afkuwar wannan bala’i tare da tabbatar wa al’ummarmu cewa za a ba da fifiko wajen kare su a ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka.
Gwamna Sani a madadin al’ummar jihar Kaduna ya mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu tare da addu’ar Allah ya sama ma wadanda suka jikkata da kuma gaggawar samun lafiya.
“Gwamnatin jihar Kaduna ta yi alhinin asarar rayuka da aka yi, kuma ta jajirce wajen ganin mazauna yankin sun ci gaba da rayuwa tare da gudanar da sana’o’insu na halal ba tare da tsoro ba.
Discussion about this post