Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa Sojojin sama sun kashe ‘yan ta’adda 4 a makon jiya.
Dakarun sun kashe Machika, Haro, Dan Muhammadu da Ali Alheri wanda aka fi Sani da Kachalla Ali Kawaje.
Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da haka ranar Asabar a Abuja.
Buba ya ce Machika ya shahara wajen haɗa bom kuma kanen gogarman ɗan ta’adda Dogo Gide sannan Haro da Dan Muhammadu sun shahara a yin garkuwa da mutane.
Ya ce Sojojin kasa da sama a ranar 11 Disemba sun kashe Kachalla Kawaje Shugaban ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da daliban Jami’ar Gusau a jihar Zamfara.
Ya ce dakarun sun kashe Kachalla tare da baradansa a karamar hukumar Munya dake jihar Neja.
Bayan haka Buba ya ce a Kudu maso Gabas dakarun tare da hadin guiwar wasu jami’an tsaron yankin sun kama kwamandan kungiyar IPOB/ESN.
Ya ce dakarun sun kama Uchechukwu Akpa tare da wasu kwamandoji uku da suka hada da Udoka Anthony Ude, Ikechukwu Ulanta da Ezennaya Udeigewere a maboyar su dake cocin katolika na ‘Christ the King’ dake kauyen Ameta Mgbowo a karamar hukumar Awgu jihar Enugu.
“Dakarun sun samu bayanin cewa Akpa tare da sauran kwamandojin na Shirin yi wa babban kwamandansu na jihar Enugu Chocho juyin mulki sannan da kai wa jami’an tsaron hari.
Buba ya ce a ranar 14 ga Disemba spjoji sun kwato bindiga kirar AK 47 da bindiga kirar pump action daya a wani harin da suka Kai wa mahara a yankin.
Ya ce a cikin makon dakarun sun kama mutum 66 barayin mai sannan sun ceto mutum 89 da aka yi garkuwa da su.
Buba ya ce a yankin Neja-Delta dakarun sun lalata rijiyoyin mai 15, jiragen ruwa 25, manyan tankunan mai 74, motoci 14, murhunan dafa abinci 115, matatar mai 64 da dai sauran su.
Ya ce dakarun sun kwato lita 357,350 na bakin mai, lita 185,300 na AGO da lita 20,600 na PMS.
Discussion about this post