Babban maƙasudin kafa hukumomin tsaro shi ne a samar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasa. To amma yanzu a Najeriya kowane ɓangare na hukumomin tsaro, ba su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da juna. Idan babu nukura, to akwai hassada. Idan babu hassada, to akwai adawa. Idan babu adawa to akwai ganin-ƙyashi. Idan babu waɗannan duk, to akwai yanken-baya a tsakanin su. Kai munin lamarin ma shi ne yadda yadda ta kan kai su ga yin fito-na-fito, har abin kan kai ga asarar rai.
Irin wannan abin takaici ne ke buƙatar a gaggauta kawar da shi ta hanyar cusa ƙwarewa a aikin tsaro ga jami’an tsaron.
Tilas idan ana son samun nasarar kawar da wannan gagarimar matsala, to fa tilas sai Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tashi tsaye, a matsayin sa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya kakaf.
Cikin Nuwamba tankiya ta tirniƙe tsakanin soja da ɗan sanda a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, har aka bindige wani Saje Jacob David. Tankiyar wadda ta faru a shingen binciken motoci kan titi, ta kai ga raunata soja ɗaya.
Daga nan ne abokan aikin sa suka garzaya barikin soja, suka tattago sojoji ‘yan uwan su, su kuma suka afka Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Yola, domin ɗaukar fansar kisan ɗan uwan su soja da ɗan sanda ya yi.
Rikicin ya yi rincimi, har sojoji suka lodin motoci 12, zaratan ‘yan kai gudummawar yin ramuwar-gayya.
Wannan mummunan al’amari ya haifar ruɗani da gudun kowa-ya-yi-ta-kan -sa a Jimeta.
Haka nan kuma irin wannan karya doka da ɗaukar doka a hannu da jami’an tsaro ke yi, ta faru a Jihar Kaduna, inda Sojojin Sama suka yi wa Ofishin EFCC dirar-mikiya, domin ƙwato jami’an su waɗanda suka je ofishin da nufin fitar da mutum biyar da ake zargi da aikata damfara da kuma zamba.
Abin mamaki ne da har Sojojin Sama za su shiga sha’anin kuɓutar da masu laifi daga hannun EFCC.
Waɗanda suka yi wannan kasassaɓar, kwata-kwata ba su dace da aikin jami’an tsaro ba. Ya kamata a gaggauta korar su daga aikin soja.
Shugaba Tinubu ya fara cin karo da irin wannan matsala, kwana ɗaya bayan rantsar da shi, inda a ranar 30 ga Mayu, sai da ta kai ya bai wa SSS umarnin su fice daga Ofishin EFCC da ke kan titin Awolowo, a Ikoyi, Legas, wanda suka mamaye ba tare da bin ƙa’ida ba.
Kafin su mamaye ofishin, sai da suka fara hana jami’an EFCC shiga ko bin hanyar zuwa ofis ɗin na su.
Irin wannan karya doka ko take doka ba ga ƙananan jami’an tsaro kaɗai ta tsaya ba. Har ma kan manyan kwamandojoji da shugabannin hukumomin tsaro daban-daban a gwamnatocin baya da wasu da ke kan aiki a yanzu.
Ya kamata dai Shugaba Tinubu ya tashi tsaye, ya kawo ƙarshen wannan matsala. Gagarimar matsalar tsaron da ta addabi Najeriya ita ce abin neman ganin jami’an tsaro sun haɗa kai sun kawar. Amma takun-saƙa da fito-na-fito ko take doka a tsakanin su, ba alheri ba ne a mawuyacin halin da ƙasar nan ke ciki.
Discussion about this post