A lokacin da suka bayyana gaban Majalisar Tarayya, Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya sun shaida wa ‘Yan Majalisa gaskiyar dalilin da ya sa matsalar tsaro ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa a faɗin ƙasar nan.
Manyan hafsoshin sun riƙa bayyana dalilan da suka sa aka kasa shawo kan matsalar tsaro, a lokacin da kowanen su ke jawabi ɗaya bayan ɗaya.
Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Musa ne ya fara jawabi. Gaba ɗayan ‘yan majalisar duk jikin su ya yi sanyi, in irin yadda shugabannin tsaron ƙasar nan ke kukan yadda matsalar ta gagara a daƙile ta.
Yayin da irin batutuwan da suka riƙa fitowa daga bakin hafsoshin tsaron abin firgici ne matuƙar gaske, to kuma sun yi namijin ƙoƙarin da har suka yanke shawarar fitowa su shaida wa duniya halin da ake ciki a Najeriya.
Sun nuna cewa duk da an shafe shekaru sama da 10 ana faman yaƙi da ta’addanci a faɗin ƙasar nan, har yanzu Kashe-kashe, garkuwa da mutane, banka wa garuruwa wuta, biyan diyya karɓo fansa, tayar da ƙayar baya, satar ɗanyen mai da sauran su har yanzu lamarin na nan da munin sa matuƙa.
Yayin da a sama ake fama da rashin gwamnati nagartacciyar, sai kuma rashin maida hankalin jami’an gwamnati da shugabanni, akwai kuma ko’ina, sannan akwai matsanancin rashawa wajen wawure maƙudan kuɗaɗen aikin samar da tsaro.
Lallai abin takaici ne matuƙa ganin yadda Hafsoshin Tsaron Najeriya su ka nuna rashin jin daɗin su ƙarara, dangane da halin rashin tsaron da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan.
Babban Hafsan Sojojin Kasar nan ya ce lamarin ya yi munin da jami’an gidan kurkuku na haɗa baki da ɗaurarrun Boko Haram, su na amfani asusun bankunan jami’an kurkukun ana tura kuɗaɗen aikata laifukan kai hare-hare.
Sannan kuma wasu lokutan Alkalai na saki Boko Haram ɗin da tsare a kurkuku, kuma duk wanda ya fita ba ya nadama, sai ya koma aikata ta’addanci.
Ƙarin abin firgici a lamarin shi ne yadda Babban Hafsan Sojojin Tsaron Ƙasa ya ce ‘yan Boko Haram ɗin da sojoji ke kamawa Alkalai na sakin su, su ka riƙa yi wa iyalan sojoji barazana. Ya ce kai har sojojin kan su ‘yan Boko Haram ɗin na yi masu barazana.
Christopher Musa ya ce yayin da malejin tsadar rayuwa ya haura kashi 27, ga masu garkuwa da ‘yan bindiga na ƙara darzazar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, to akwai babbar barazana sosai a ƙasar nan, musamman ganin yadda noma ya gagara a yankunan nan da dama.
“Jama’a na fama da yunwa. Duk irin yadda za ka ce masu su zauna lafiya, ba za su saurare ka ba, saboda sai sun ci za su yi tunanin zaman lafiya. Yunwa kuwa na ƙara dugunzuma aikata muggan laifuka.” Inji Musa.
Yadda ake shiga da fita sakaka a kan iyakokin Najeriya da Nijar, Najeriya da Kamaru da Najeriya da Jamhuriyar Benin, abu ne da a kullum ke ƙara munana matsalar tsaro.
Musa ya ce akwai kan iyakoki kamar kilomita 4,000 a faɗin ƙasar nan. Daga cikin su, kilomita 1,600 duk kan iyakokin mu ne da ƙasashen yankin Sahel, inda ta nan ake tururuwar shigo da manyan bindigogi, kuma sama da shekaru goma kowa ya san wannan.
Ya ce ta hakan ana barin ƙofofin da ake taimaka wa ‘yan Boko Haram da ISWAP da sauran ‘yan bindiga ƙoƙarin su na neman tarwatsa Najeriya.
Irin yadda Arewa ke fama da matsalar tsaro, haka su ma can Kudu na fama da nasu matsalolin.
Shi kuma Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja, ya shaida wa Majalisar Tarayya cewa, “sojoji fa ma wasu matsafan da za su iya yin wani siddabaru ba ne.” Lallai maganar sa haka ta ke. Domin kowa ya san aiki ya yi wa sojojin Najeriya yawa, ganin yadda zaratan sojojin Najeriya ke aikin samar da tsaro a wurare daban-daban cikin jihohi har 33, daga cikin 36 da muke da su. Kuma dukkan wannan aikin da su ke yi, ba wajibcin su ba ne, aiki ne na jami’an ‘yan sanda da sauran ɓangarorin tsaron cikin gida.
Shi kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, kukan ƙarancin jami’an ‘yan sanda ya yi. Cewa ya yi adadin yawan su baki ɗaya idan aka ɗora kan sikeli, duk ɗan Najeriya 1,000 zai samu kulawar ɗan sanda 1.
Sai dai abin dariya shi ne yadda ya ƙi yin magana kan yadda sama da ‘yan sanda 100,000 na can na tsaron shugabanni da manyan ‘yan siyasa da sauran masu ƙumbar susa.
Akwai dibijin na ‘yan sanda guda 1,537 a ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan. Kowane ofishi ba shi da kwarjinin da za a ce ofishin jami’an kula da tsaro ne.
Abin fa ya na da yawa, wai mutuwa ta je kasuwa. Ɓangaren Sojojin Sama da Sojojin Ruwa kowane na fama da nasa matsalolin.
Gaskiya akwai jan aikin da ya zama dole a tashi tsaye a kawar da matsalar tsaro, kafin matsalar tsaro ta sa kowa kwana a tsaye.
Discussion about this post