Cincirindon Matasan Arewa a ƙarƙashin Ƙungiyar Arewa Youth Movement, sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, inda su ke kira da a gaggauta tsige Ministan Harkokin Tsaro, Badaru Abubakar.
Kungiyar wadda ranar Laraba suka yi dafifi bakin ƙofar shiga harabar Majalisar Ƙasa a Abuja, sun ce kwata-kwata ba su gamsu da irin riƙon-sakainar-kashi da Badaru ke yi wa matsalar tsaro, musamman a Arewa ba.
Masu zanga-zangar su kimanin 100, su na ɗauke da kwalaye da takardu da aka yi wa rubutu daban-daban, masu ɗauke da saƙon nuna rashin cancantar Muhammad Badaru a matsayin Ministan Tsaro.
Wasu kwalayen na ɗauke da rubutu kamar haka: “Badaru ka tashi daga barci haka nan”, “Wai ina Badaru ya shige ne?, da sauran su.
Wannan fushin na su ya biyo bayan kisan da Sojojin Najeriya suka yi wa fararen hula 85 da jikkata fiye da 100 a ƙauyen Tudun Biri, cikin Ƙaramar Hukumar Igabi, a Jihar Kaduna, a ranar Asabar da dare.
Ba wannan ne karo na farko da sojoji suka kashe fararen hula a ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci ko ‘yan bindiga ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga Jadawalin Garuruwan Da Sojoji Suka Jefa Bamabaman da Suka Ɗaruruwan Fararen Hula.
Kisan Musulamai masu halartar taron Maulidi su 85, tare da jikkata mutum fiye da ɗari wanda Sojojin Najeriya su ka yi a bisa ‘tsautsayi’, ba shi ne na farko ba.
Kisan wanda aka yi a ƙauyen Tudun Biri cikin Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Katsina, ya tada hankulan jama’a da dama. Kuma ana ta kira ga Sojojin Najeriya da Gwamnatin Najeriya cewa a yi bincike, a hukunta sojojin da suka jefa bamabaman, a kuma biya diyyar waɗanda aka kashe da waɗanda aka jikkata.
Jihar Nassarawa: Farar Hula Sama Da 40:
Cikin Janairu 2023 an kai irin wannan hari kan jirgin da ba matuƙi a Jihar Nassarawa, har aka kashe makiyaya 27.
Amma dai Fulani makiyaya sun ce waɗanda aka kashe ɗin sun kai 40.
Waɗanda aka kashe ɗin dai Fulani ne waɗanda ke kan hanyar su ta komawa ruga, bayan sun karɓo shanun su da Gwamnatin Jihar Benuwai ta kama.
Jihar Zamfara: Farar Hula Sama Da 70
Irin wannan mummunan hari kan farar hula ya faru a Jihar Zamfara, a cikin 2022, a cikin yankin Ɗansadau da ke cikin Ƙaramar Hukumar Maru.
Sojoji sun kai farmakin kakkaɓe ‘yan bindiga a ƙauyen Matunji, sai dai kuma bam ɗin da aka jefa ta sama jirgin yaƙi, ya yi kisan kai-mai-uwa-da-wabi, domin an kashe farar hula sama da 70.
Katsina: Farar Hula 6:
Cikin Yuli, 2022 aka kashe mutum 6 a yankin Kunkunna, cikin Ƙaramar Hukumar Safana. Sojojin Sama ne suka jefa bam dagakam Jirgin Yaƙi samfurin Jet.
Jihar Neja: Yara Ƙanana 6:
Cikin Afrilu 2022, Sojojin Sama sun kashe yara shida masu ɗibar ruwa a rijiyar tsakiyar ƙauyen Kurebe, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro.
Abin takaici, ‘yan bindiga ne suka kashe iyayen yaran da Sojojin Saman Najeriya suka jefa wa bam a cikin 2020.
Jirar Barno: Kisan ‘Yan Gudun Hijira 52:
Cikin watan Janairu, 2017, Sojojin Sama sun jefa bam a Sansanin Masu Gudun Hijira a ƙauyen Rann, suka kashe mutum 52, suka raunata 120. Ƙauyen Rann ya na cikin Ƙaramar Hukumar Kala-Balge a Jihar Barno.
Tun daga kisan na 2017, har zuwa yau, duk da ana cewa a yi bincike, amma har yau shiru ka ke ji.
PREMIUM TIMES ta kira wayar Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, bai ɗauka ba. An tura masa tes shi ma bai maido amsa ba, ballantana a yi halin da ake ciki, dangane da binciken kashe-kashen da sojoji suka ce za su yi a baya.
Discussion about this post