Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya rage wa matafiya hutun Kirsimeti da sabuwar shekara kuɗin motocin sufuri da kashi 50 bisa 100 a garuruwa daban-daban cikin faɗin ƙasar nan.
Tinubu ya kuma bada umarnin cewa a shiga jiragen ƙasa kyauta daga ko’ina zuwa ko’ina a faɗin ƙasar nan.
Umarnin hawa jirgin ƙasa kyauta da kuma biyan rabin kuɗin shiga motocin sufuri, zai fara ne daga ranar Alhamis, 21 ga Disamba zuwa 4 ga Janairu, 2024.
Wannan umarni ya fito ne daga bakin Ministan Albarkatun Ƙasa, Dele Alake, yayin da ya ke wa manema labarai jawabi a Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Laraba.
Ya na tare da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris da kuma Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, a lokacin da ya ke masu jawabin.
Haka kuma a wurin akwai Mashawarcin Musamman na Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga.
Alake wanda shi ne Shugaban Kwamitin Rage Kuɗaɗen Sufuri lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara, ya ce tuni har kwamitin sa ya gana da shugabannin ƙungiyoyin masu motocin sufuri da direbobi a faɗin ƙasar nan, kuma sun cimma yarjejeniyar cewa Gwamnatin Tarayya ce za ta biya su cikon kashi 50 bisa 100 da za a rage wa matafiya.
Sai dai kuma ya ce babu zirga-zirgar jiragen sama a wannan sassaucin da aka yi na zirga-zirga, saboda maƙasudin sassaucin shi ne a yi wa talakawa rangwame.
“Daga ranar Alhamis gobe, fasinjoji masu barin wata jiha zuwa kowace jiha da Abuja, Legas, Kaduna, Enugu, Fatakwal, Owerri, Ibadan, Akure, Maiduguri, Sokoto da sauran manyan jihohin zirga-zirga, za su riƙa biyan kuɗin mota, sauran rabin kuma gwamnatin tarayya ce za ta biya masu.
“Kuma Shugaban Ƙasa ya yi magana da sashen ‘yan sanda, SSS da Sojojin Najeriya cewa su tabbatar matafiya sun yi zirga-zirgar su lami lafiya.”
Tun a ranar Talata ce dai Shugaba Tinubu ya yi albishir cewa zai rage wa matafiya kuɗin mota, domin rage masu tsadar rayuwa da tsadar kuɗin mota, a lokacin tafiya hutun Kirsimeti da na Sabuwar Shekara.
Ya yi albishir ɗin yayin ganawar da da Shugabannin Ƙungiyar Masu Gidajen Jaridu ta Najeriya (NPAN).
Discussion about this post