Gwamnatin Kano ta siya kayan yin gwajin cutar kanjamau na naira miliyan 69 domin dakile yaduwar cutar a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Labaran Yusuf ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai domin ranar cutar kanjamau ta duniya da aka yi a garin Kano ranar Juma’a.
Yusuf ya ce gwamnati ta raba kayan gwajin cutar ga asibitoci 590 domin kawar da matsalar rashin kayan yin gwajin cutar.
Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin cimma burin ta na yi wa mutum kashi 95% gwajin cutar nan da shekarar 2025.
Yusuf ya ce ma’aikatar kiwon lafiya da hukumar dakile yaduwar cutar ta jihar SACA za su ci gaba da hada hannu domin ganin an samar wa duk masu fama da cutar taimakon da suke buƙata.
Ya ce gwamnati ta kashe naira miliyan 5.9 wajen samar wa masu fama da cutar magunguna a Kano.
“A wannan taro Jihar Kano na tare da mutum miliyan 38 a duniya da mutum sama da miliyan biyu dake fama da cutar da wadanda cutar ta yi ajalinsu.
Ya ce tare da taimakon SACA da USAID – LHSS gwamnati ta saka mutum sama da 600 cikin tsarin BHCPF.
Yusuf ya ce mutum 4,728 daga cikin mutum 138,430 din da aka yi wa gwajin cutar daga Janairu zuwa yanzu sun kamu da cutar inda zuwa yanzu wadannan mutane na amsar maganin cutar kyauta a asibitocin jihar.
Discussion about this post