Zancen da ya mamaye dukan ƙasashen duniya, ta hanyar tattaunawa mai zafi, tsakanin magoya bayan ɓangarori biyu: na Falasɗinawa, da na Isra’ilawa, shi ne: cigaba da abubuwan baƙin- ciki, da kwararar jini a Falasɗin na tsawon watanni biyu da suka shuɗe, tattaunawa ce mai zafi da dukan kafafen yaɗa labarai na duniya suka duƙufa gabatarwa. Wannan tattaunawar ta bankaɗo cewa: lallai rashin sanin tarihi, da kuma rashin sanin inda asalin abin ya taso, shi ne babban abin da yake yin jagora zuwa ga shi kansa tattaunawar, abin ya fito fili ƙarara ta hanyar tambayar da ake yi na cewa: mene ne ya sanya wannan abu ya faru? Ma’ana abin da ya faru a ranar 7 ga watan Oktoba.
Taƙaitacciyar amsa a nan ita ce: mulkin mallaka, da kuma rasa duk wani yunƙuri na haƙiƙa wajen samar da zaman lafiya. Wannan taƙaitacciyar amsa ta yi kama da mutumin da ya sha ruwan kogi, za ka same shi yana matuƙar neman ƙari, al’umma suna matuƙar buƙatar ilimi, da ƙarin bayani game da ita, amsa ce taƙaitacciya, da ita kanta take haifar da wata tambayar cewa: to wane ne za a ɗaura wa laifin rasar da samar da wannan yunƙuri na zaman lafiya na haƙiƙa?
A ra’ayin duk wani mai zurfafa bincike, da ya san siyasa, yake kuma aiki da hankali gami da sanin- ya- kamata, wanda bai ɗauki ɓamgaranci ba, lallai kowa ya san cewa Isra’ila ce za ta ɗauki wannan laifin, lura da dalilai masu yawa, bari mu kawo wasu daga cikinsu:
Bayan an rattaba hannu a yarjejeniyar Oslo, ƙungiyar neman ‘yancin Falasɗinawa, ƙarƙashin jagorancin marigayi Yasir Arafat, ta shiga cikin shirin samar da zaman lafiya na haƙiƙa, da manufar kafa daular Falasɗinawa a ƙasar Falasɗinu, da aka yi mata mulkin mallaka, tun shekarar 1967, wadda ba ta wuce kashi 22% kacal na asalin faɗin ƙasar Falasɗinu ba, akan gabashin garin Ƙudus ya zama nan ne babban birnin wannan sabuwar ƙasa ta ake shirin kafawa. Bugu da ƙari kuma, a warware matsalar ‘yan gudun hijiran Falasɗinawa, ƙarƙashin ƙuduri na 194, da ta yi na’am da shi a ranar 11 ga watan Satumba 1948.
Idan muna magana game da samar da ƙasashe guda biyu a matsayin mafita, ba wani sabon abu ne muka kawo ba, wannan mafita ne da take ƙunshe a cikin ƙudurin majalisar ɗinkin duniya mai lamba 181, tun shekarar 1948, ƙudurin da aka fi sani da sunan “ƙudurin raba Falasɗin”, muna iya cewa wannan ne “certificate” ɗin haihuwar wannan mafitar, da kamata ya yi a ce ya faru a tun wancan lokaci. Ey, an kafa ɗaya daga cikinsu, wato ƙasar Isra’ila, haihuwar ɗayan kuma ya zo da tangarɗa, domin shekaru 77 kenan ana naƙuda, ba a kai ga haihuwarta ba, watau Falasɗin. Sannan ba wai matsalar ta ƙuduri mai lamba 181, ko sabunta kawo mafitar kafa ƙasashe guda biyu ba ne kwata- kwata, matsalar ita ce rashin samun cikakkiyar niyya daga ƙungiyar ƙasa da ƙasa, wannan matsalar ce ta hana haihuwar wannan ƙasa ta biyun har zuwa yau.
Tun ranar da aka kafa ƙasar Isra’ila ba ta taɓa yin ƙasa- a- gwiwa ba wajen kawo cikas akan duk wata dama ta kafa ƙasashe biyu, ta fara da ƙin zartar da ƙudurin babban zauren majalisar ɗinkin duniya mai lamba 181, haka ma da ƙuduri mai lamba 194, wanda ya yi kira zuwa ga komawar ‘yan gudun hijiran Falasɗinawa zuwa gidajensu, waɗanda aka kore su daga ƙasarsu ta asali, sannan kuma ta ƙara tabbatar da hali, gami da yanayin Falasɗinawa a ƙasashen da suka tarwatsu, abin da ya ƙara wa Barno- dawaki kuma, shi ne Isra’ila ta ƙara mamaye sauran ƙasar Falasɗin da ta rage, wadda take akan iyakar da aka shata a watan Yuni, na shekarar 1967, har ma da yankin tsibirin Saina’a na ƙasar Misra, da Tuddan Gulan na ƙasar Siriya.
Bayan kawo cikas da Isra’ila take yi a wajen zartar da ƙudurin kafa ƙasashe guda biyu, da samar da ƙasar Falasɗin a kaso 22% na faɗin ƙasarta na asali, ita dai Isra’ilar ba ta tsayar da gine- ginen da take yi a ƙasar Falasɗin ba, tun sanda ta fara mulkin mallakar da take yi, shi kuwa waɗannan gine- gine da take yi a ƙasar Falasɗin, da kafa ƙasar Falasɗin abubuwa ne kaman ruwa da wuta, ba za su taɓa haɗuwa a wuri ɗaya ba har abada. Mafitar kafa ƙasashe biyu yana nufin: rusa gine- ginen unguwanni da Isra’ila ta yi a ƙasar Falasɗin, wanda da ma hakan karya dokokin ƙasa da ƙasa ne ƙarara, sannan ta kuma janye ta koma kan iyakar da aka shata a shekarar 1967, har ƙasashen Turai da suka goyon bayan Isra’ila ba tare da lissafi ba, sun bayyana waɗannan gine- ginen unguwanni da take yi a matsayin babban cikas a yunƙurin da ake yin a tabbatar da zaman lafiya, da kafa ƙasashe guda biyu.
Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana cewa gina wuraren da suke na Falasɗinawa ne, ya fara ne tun a makon farko na fara mulkin mallaka, inda suka mamaye gabashin Ƙudus a shekara ta 1967, lokacin da Isra’ila ta rusa gidaje 160 a Unguwar al- Maghariba a tsohon garin Ƙudus, wanda suke daura da katangar yammancin Masjidul Aƙsa, wurin da aka fi sani da “Ha’iɗul Buraƙ”, haka ma da ƙwace wasu gidajen har guda 600, bayan sun fitar da mazauna cikinsu na asali da suka kai mutane 5500.
Ƙungiyar samar da zaman lafiya kuwa, wadda ƙungiya ce a ƙasar Isra’ila, wadda ba ta gwamnati ba, ta bayyana cewa: a daidai lokacin da aka rattaba hannu a yarjejeniyar Oslo a shekarar 1993, akwai kusan ‘yan- kama- wuri- zauna dubu 250 a West Bank, abin da ya haɗa har da gabashin Ƙudus, da suke rayuwa a unguwanni 140 da Isra’ila ta gina a ƙasa Falasɗin, a yanzu kuwa alƙalumman sun ƙaru, inda ‘yan kama- wuri- zauna dubu 700, da suke rayuwa a unguwanni 300 da Isra’ila ta ƙwace ta gina masu, wannan yana nufin cewa akwai ƙari da kaso 280% na adadin ‘yan kama- wuri- zauna, da kuma ƙarin 210% na adadin unguwanni da aka gina.
Idan muka yi la’akari da alƙalumman da suka gabata a sama, to da baban murya za mu iya cewa: duka gwamnatocin Isra’ila da suka zo a tsawon shekaru talatin da suka gabata, ba su da niyyar dakatar da mulkin mallakar da suke yi, sun kuma yi nasarar samar da wani yanayi na ƙasa guda ɗaya, wadda ta ginu akan wariya, wanda abu ne mai matuƙar wuya a kawo ƙarshen wannan yanayin, sun bar Falasɗinawa a teburin tattaunawa, hannu- Rabbana, ba su da komai a hannunsu da zai kai su zuwa ga kafa ƙasarsu.
Gine- ginen unguwanni da Isra’ila ta yi a ƙasar Falasɗin ba shi ne cikas na ƙarshe da Isra’ila ta gicciya a hanyar shirin aiwatar da mafitar samar da ƙasashe biyu ba, domin tun ranar da Natanyaho ya ɗare kan karagar fira-minista ya gindaya sharaɗin da sai ya tabbata sannan zai yarda ya a zauna a teburin tattaunawa, wannan sharaɗi kuwa shi ne: a amince da Isra’ila a matsayin ƙasa ce ta Yahudawa, kuma wai Ƙudus nan ne Babban barnin Yahudawa na har abada.
Abin mamaki a cikin wannan al’amari shi ne: lokacin da ƙungiyar neman ‘yancin Falasɗin ta yarda ta rattaba hannu a yarjejeniyar Oslo 1993, wanda ya rattaba hannu da sunan Isra’ila, wanda shi ne fira- mininstanta Ishaƙ Rabin ya rattaba ne da sunan ƙasar Isra’ila, ba ƙasar Yahudawa ba, haka ma lokacin da Isra’ila ta rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da Misra, da Jordan, duka sun rattaba hannu ne da sunan ƙasar Isra’ila, ba ƙasar Yahudawa ba. A baya – bayan nan ma da wasu daga cikin ƙasashen Larabawa suka yi yarjejeniyar kyautata dangantaka da Isra’ila, an rattaba hannu ne da suna ƙasar Isra’ila, ba da sunan hukumar al’ummar Yahudawa, ko ƙasar Yahudawa ba, kawai suna neman dole ne sai Falasɗinawa su sauya tsohuwar yarjejeniyar da suka yi da su, ya zama sun yarda da su a matsayin ƙasar Yahudawa, sun riga sun san cewa hakan ba abu ne da zai taɓa yiwuwa ba, saboda dalilai na kishin ƙasa, da na tarihi, wanda sharhinsu a nan zai yi tsawo, saboda haka neman a ce sai Falasɗinawa sun yi i’itirafi da Isra’ila a matsayin ƙasar Yahudawa, wani babban gungume ne da yake kawo cikas a yunƙurin samar da zaman lafiya.
Idan mun cimma wannan matsaya; -wannan shi ne abin da ya ginu akan aiki da hankali- na cewa Isra’ila ita ce take da laifin daƙile duk wani yunƙuri na samar da zaman lafiya a ƙasa mai tsarki, to wannan ma zai miƙa mu zuwa ga wata tambayar, wadda ita ce: to mene ne mafita? Mene ya kamata a yi domin tabbatar da zaman lafiya?
Ku ɗin nan a matsayinku na al’ummar duniya, da shugabannin addinai, da shugabannin siyasa, da masu tasiri a cikin rayuwar zamantakewa, da shugabannin ƙungiyoyin sa- kai, da masu tasiri a shafukan sadarwa na zamani, da ‘yan jarida, da hukumomin gwamnati, da waɗanda ba na gwamnati ba, da sauransu, cikin hukumomi, da cibiyoyi, kai har ma da fitattun mutane; lallai dukan ku kuna da rawar da za ku taka a tare, kowa daga cikinku yana da rawar da zai taka a kewayensa, da zai iya kawo sauyi a cikin yanayin da ake ciki.
Bari mu tuno da goyon bayan da muka nuna gaba ɗayanmu, da ma abubuwan da muka yi amfani da su wajen kawo ƙarshen mulkin wariya a ƙasar Afrika ta Kudu (South Africa), gaba ɗayanmu a lokacin mun haɗa- kawunanmu, kuma mun yi nasara wajen yi wa siyasar wariya, da fifita farare akan baƙaƙe burki, lallai lokacin da kanmu yake a haɗe, mun iya kawo sauyi na haƙiƙa.
A waɗannan kwanakin na sheƙar da jini ma, za mu iya yin amfani da wannan kisan- kiyashin da yake faruwa, wajen yi wa gwamnatin mulkin mallaka ta Isra’ila matsin- lambar ta dawo kan teburin tattaunawa; har abada Isra’ila ba za ta dawo kan teburin tattaunawa da sonta ba, ba ku buƙatar in faɗa maku cewa kuna da abubuwa masu yawa da za ku iya yi, wajen tirsasa wa gwamnatil mulkin mallaka dawowa kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya.
Lallai yanzu ne lokacin da ya fi dacewa a yi kira, da matsin- lamba ga ƙasashen Turai, da su dakatar da bai wa Isra’ila kariyar da take hana dokokin ƙasa da ƙasa yin aiki akanta, su dakatar da goyon- baya, da tallafi marasa iyaka da suke ba ta, lallai yanzu ne lokacin da ya dace a kawo ƙarshen siyasar ‘yar mora, da ‘yar bora, da siyasar awo da ma’aunai guda biyu da suka saɓa da juna.
Ina ganin cewa yanzu ne lokacin da za dakatar da yin mu’amala da Isra’ila a matsayinta ƙasar da ta fi ƙarfin dokokin ƙasa da ƙasa, da take samun cikakkiyar kariya ga barin dukan hukunce- hukuncen da aka tanadar ga duk wanda ya karya dokokin ƙasa da ƙasa, ko ya yi wasti da ƙudurorin majalisar ɗinkin duniya.
Bari mu yi amfani da jinin dubban mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, wajen haskaka wannan hanya ta siyasa da za ta kawo ƙarshen wannan raɗaɗin da ya ƙi ci, ya ƙi cincewa.
A taƙaice, lallai wannan abu ne da zai iya faruwa idan muka daina mu’amala da Isra’ila a matsayin ‘yar lelen ƙasa shagwaɓaɓɓiya da ta fi ƙarfin doka.
Abdullahi Muhammad Abushawesh
Jakadan Falasɗin a Najeriya
Discussion about this post