‘Yan Majalisar Tarayya sun yi zargi mai cike da abin mamaki da al’ajabi cewa, gafakar kundin kasafin 2024 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar masu, fanko ne a ciki, babu kwafe-kwafen kundin a cikin gafakar.
Sashen Hausa na BBC ya rubuto cewa “bikin gabatar da kasafin kuɗin a Najeriya da shugaban kasar ya yi ga Majalisar Dokoki ya bar baya da ƙura, inda wasu `yan majalisar ke zargin cewa shugaban ƙasar ya yaudare su inda suka ce ya miƙa musu kundin ƙudurin kasafin kuɗin 2024 na bogi.”
Rahoton ya ci gaba da cewa, “a ranar Laraba ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da ƙudurin kasafin kudin sa na farko ga zaman hadin gwiwar Majalisun Najeriya.
“Shugaba Bola Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin na shekara mai zuwa ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur ɗaya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum. Sannan da dalar Amurka daya a kan canjin naira 750.
Kasafin kudin ya yi kudurin kashe naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum. Sai kuma naira tirliyan 8.25 wajen biyan bashi, yayin da manyan ayyuka za su samu naira tirliyan 8.7.
“Sai dai ‘Yan Majalisar sun ce “babu komai a cikin wani dan akwatin da shugaban kasar ya rusuna ya ajiye a gaban zauren majalisar.”
Yusuf Shitu Galambi, ɗan majalisar wakilan Najeriya, ya shaida wa BBC cewa ko shakka babu shugaban kasa ya karanta musu jawabinsa na kasafin kuɗi, amma maganar kundi na kasafin kuɗin ba su ganshi ba.
Ya ce, “Shugaban ƙasa ya karanta mana lissafe lissafen kuɗin, to amma gundarin yadda kasafin yake na kowacce ma’aikata kamar yadda aka saba yi ba a kawo shi ba.”
Ɗan majalisar ya ce,” Mun duba kundin da ya ajiye amma ba mu ga komai a cikin sa ba.”
Galambi, ya ce a tarihin majalisar wakilai ta tarayya ba a taɓa irin abin da aka yi ba a wannan karon, kuma kundin tsarin mulki ba haka ya ce a yi ba.
Ya ce, “Mu kanmu ‘yan majalisar wannan abu ya ɗaure mana kai, saboda abu ne wanda ba a taɓa gani ba sannan ba a taba zata ba ko a mafarki.”
“Muna ganin wannan abu kamar yaudara ce.” Inji shi
PREMIUM TIMES Hausa kuwa, ta buga labarin inda jam’iyyar PDP ta roƙi ‘yan majalisa cewa, ‘ku yi watsi da kasafin 2024, cike ya ke maƙil da almara, tatsuniya, aringizo, rufa-rufa da lissafin-dokin-Rano”.
Babbar Jam’iyyar adawa, PDP ta riƙi Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa cewa kada su amince da kasafin 2024, domin cike ya ke maƙil da aringizo, almara da rainin hankali ga talakawa.
Sakataren PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Litinin, jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya kammala gabatar da kasafin a gaban gamayyar zauren Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya, a Abuja a ranar Laraba.
Kasafin na Naira tiriliyan 27.5 dai PDP ta ce akwai rufa-rufa damƙam a cikin sa.
Don haka ta roƙi majalisa ta yi amfani da Kundin Dokokin Najeriya Sashe na 80, 81 da 82 na 1999 su watsar da kasafin.
PDP ta ce maimakon majalisa ta yi amfani da kasafin mai cike da shifcin-gizo, ta yi watsi da shi ta hanyar bijiro da kasafin da zai amfana wa talaka da tattalin arzikin ƙasar nan baki ɗaya.” Haka Ologunagba ya bayyana.
“Saboda a cikin kasafin akwai rufa-rufa, shifcin-gizo, lissafin-dokin-Rano da kuma uwa-uba aringizon maimaita wasu ayyuka da dama sau biyu.”
Ya ce batutuwa da dama da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bijiro da su a cikin kasafin na 2024, ba za a iya aiwatar da su ba, saboda an ƙirƙiro su ne a kan hasashen da aka yi wa kirdado bisa ta hanyar yin amfani da alƙaluman ƙididdigar lissafin dokin Rano.”
Ya ce kasafin cike ya ke da buƙatun kashe maƙudan kuɗaɗe wajen samar da kayan alatun jin daɗin more rayuwar shugaban ƙasa, wanda tun tuni ya ke mafarkin samu, sai yanzu dama ta samu.
Ya ce ba daidai ba ne kasafi ya ta’allaƙa wajen kashe biliyoyin kuɗaɗen da za a ciwo bashi ana narka wa wajen holewar shugaba, shi kuma talaka an bar shi cikin gaganiya da tsadar rayuwar da shugaban ya jefa shi a ciki.
Discussion about this post