Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa akalla mutum 75 ne ke kwance a asibitocin Barau Dikko da Asibitin 44, sannan mutum 86 sun rasu a wannan hari.
Da ya ke hira da Talbijin din Arise Uba ya tabbatar wa ƴan Kaduna cewa ba musulmai bane kawai suka rasu. Akwai Kiristoci Uku da suka rasu a harin Tudun Biri.
” Da kai na za a biya kuɗin diyyar waɗanda suka rasu, babu wanda za a sa a gaba wai ya tattauna tsakanin gwamnati da wadanda abin ya shafa.
” Mu a jihar Kaduna babu maganan kiyayyar juna kan addini yanzu. Ƙarƙashin jagoranci na kowa ɗan jihar Kaduna ne kuma dulkan mu ɗaya ne.
” Tun da wannan hari ya auku ba mu zauna va a Gwamnatance. Ta tattauna da shugabanka, na tattauna da mataimakin shugaban kasa da sauran hafsoshin tsaron kasa. Kuma gaba ɗayan mu muna tare ne a wuri daya ne game da wannan hari.
Mataimakin shugaban kasa ya ziyarci Kaduna ranar Alhamis domin ziyara gani da Ido, abinda ya auku da irin matsalolin da wadanda abin wannan ibtilai ya afka wa suke ciki
Kashim Shettima ya ce lallai gwamnati za ta biya diyyan waɗanda suka rasa rayuka a wannan hari, kyma za a gudanar da bincike akai.
Discussion about this post