Akalla yara bakwai ne daga jihar Bauchi Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya mika su ga iyayensu a ranar Juma’a, bayan an kuɓutar da su daga waɗanda suka sace su.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata kungiyar masu garkuwa da mutane da safarar yara a tsakanin jihar tare da kama wasu mutane tara bayan shafe watanni suna bin diddigi a fadin jihohi bakwai.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ce ta fara gudanar da binciken bayan sun samu rahotan bacewar wasu yara.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Husseini Gumel, ya shaida wa manema labarai a Kano, babban birnin jihar cewa kungiyar ta shafe sama da shekaru 10 tana gudanar da ayyukanta, kuma an yi zargin ta kware wajen safarar kananan yara da kuma siyar da kananan yara a tsakanin jihohin.
Ya ce a dalilin bincike mai zurfi da aka yi ya taimaka wajen bankaɗo ayyukan kungiyar da ke da mambobi a jihohin Kano da Bauchi da Gombe da Legas da Delta da Anambra da kuma Imo.
Gwamna Yusuf, wanda ya zubda hawayen farin ciki sakamakon abin yabawa kokarin da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi, ya bayyana jin dadinsa da aikin da suke yi.
Sai dai gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka gano yara bakwai da aka sace daga jihar Bauchi sannan aka yi safararsu da sayar da su a jihohin Anambra da Legas.
Bayan haka gwamnatin Kano ta baiwa uaran da aka kubutar, naira 500,000 kowannen su, su huta gajiya.
Discussion about this post