Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa, an samu raguwar mace-mace sakamakon cutar kanjamau (AIDS) da kashi 70 a faɗin duniya tun 2004.
Majalisar ta ce duk da wannan matsayi da aka cimma, har yau AIDS na kashe mutum guda a cikin duk minti guda.
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres ne ya bayyana haka cikin saƙon da ya fitar albarkacin Ranar Yaƙi da AIDS ta Duniya ta 2023.
António Guterres ya ce, “ya zama wajibi mu ga bayan AIDS a matsayin ƙalubale ga lafiyar al’ummar duniya ya zuwa 2030.”
Ya ƙara da cewa, domin kawar da AIDS dole ne a maida hankali kan ƙauyuka wajen ba su kulawar da ta dace game da kiwon lafiya da dai sauran tallafi.
Haka nan, ya ce don cimma nasarar yaƙi da HIV ya zama dole a tafi tare da shugabanni al’ummomin karkara wajen gudanar da harkokin yaƙi da cutar.
Ya ce ana buƙatar sama da Dala biliyan takwas duk shekara wajen yaƙi da wannan cuta a ƙasashe masu samun ƙarami da matsakaicin kuɗin shiga.
“Lallai kawar da AIDS abu ne mai yiwuwa. Mu ƙarasa aikin kawar da cutar ta hanyar tallafa wa ‘yan karkara wajen yaƙi da wannan cuta,” in ji António Guterres.
Discussion about this post