Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya bayyana cewa ko kaɗan jam’iyyar PDP a jihar ba ta tsoron yin zaɓen ‘inkwankulusib’, domin al’ummar jihar sun yi amanna da gwamnatin sa da salon mulkin sa.
“Ba tsoron sake zaɓen ‘inkwankilusib’. Al’ummar Zamfara sun yi amanna da gwamnatin mu. Kuma sun damƙa mana amanar ƙuri’un su. A shirye muke da sake yin nasara. Kai ko gobe a ja daga, mun shirya tafiya zaɓen Ƙaramar Hukumar Maradun.”
Gwamna Lawal ya yi wannan jawabin ne a lokacin da dandazon magoya baya suka yi gangamin tarbar sa, lokacin da ya koma Gusau babban birnin jihar, daga wani taro da gwamnonin Arewa maso Yamma suka halarta a Abidjan, babban birnin Cote d’Ivoire.
Dubun-bubatar jama’a suka tarbi gwamnan, waɗanda suka yi masa jerin gwanon kwamba ɗin motoci, tun daga kan iyakar Ƙaramar Hukumar Tsafe, har Gusau.
Gwamna Lawal na wajen taro Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce ta soke zaɓen sa, sai an sake zaɓen ‘inkwankilusib’ a ƙananan hukumomi uku, ciki kuwa har da Maradun, mahaifar tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, wanda Lawal ya kayar a zaɓen gwamna.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Lawal, Suleiman Bala Idris ya sa wa hannu kuma ya fitar, ya ce cincirindon mutsnen da suka tarbi gwamnan alama ce kuma hujja mai cike da nunin cewa al’ummar jihar sun ba shi amanar jagorancin su a ƙarƙashin gwamnatin sa.
“Zamfarawa sun nuna wa tawagar Gwamna Lawal ƙauna idan aka dubi irin dandazon jama’ar da ta tarbe shi, tun daga Tsafe har zuwa cikin Gusau, alama ce mai nuni da irin amanna da amanar da suka damƙa wa Gwamnan.
“Muna kan hanya ɗoɗar wadda za mu ceto Jihar Zamfara, kuma babu wani tarnaƙin da zai iya kawo mana cikas wajen cimma wannan ƙudiri da alƙibla.”
Discussion about this post