Babban Hafsan Sojin kasa (COAS), Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya bayyana cewa a karkashin shugabancin sa zai tabbatar da ganin an inganta aikin soja ta hanyar ba dakaru kula ta musamman a lokacin aikin su.
Lagbaja ya fadi haka ne a taron ‘Regimental Sergeant Majors (RSMs)’ da aka yi a Ibadan jihar Oyo ranar Litinin.
Ya ce zai mai da hankali wajen kirkiro manufofin da za su ƙarfafa gwiwowin jami’an tsaron domin ganin sun gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.
Lagbaja ya yi kira ga sojojin da suka halarci taron da su cigaba da mara masa baya ta hanyar yin da’a da kuma tabbatar da cewa an ci gaba da kiyaye al’adu da da’a na rundunar sojojin Najeriya.
Ya ce yana sa ran cewa abubuwan da sojojin suka koya zai taimaka wajen inganta aiyukan dakarun a kasar nan.
Babban darektan aiyukka Jimmy Akpor, ya ce kamata ya yi a rika horas wa da wayar da kan sojoji kan sabbin manufofi da tsare-tsare na Sojojin Najeriya.
Akpor ya yi kira ga RSMs da su yi amfani da abin da suka koya a taron domin inganta halayen sojoji a sassa daban-daban a rundunar.
Discussion about this post