Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ko kaɗan ba ta baddala alƙaluman sakamakon zaɓen da ta aika a Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta IReV ba.
INEC ta ce ta lura da wasu rahotanni da ta riƙa cin karo da su a kafafen yaɗa labarai, inda ake zargin ta da hargitsa sakamakon zaɓen da ta tura a manhajar IReV, na zaɓen gwamnan Jihar Kogi.
Kogi na ɗaya daga cikin jihohi uku da aka yi zaɓen gwamna, a ranar 11 ga Nuwamba. Sauran jihohin biyu su ne Imo da Bayelsa da ke Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.
Cikin sanarwar da INEC ta fitar a ranar Talata, ta roƙi jama’a su yi watsi da zargin wai hukumar ta baddala sakamakon zaɓen da ta loda a manhajar IReV.
Ta bayyana cewa wannan zargi da aka yi wa hukumar “ƙage ne kawai da ƙarairayin bugar da hankulan jama’a.”
Wannan kakkausan martani na INEC na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kwamishinan Tarayya na hukumar, Mohammed Haruna ya fitar a ranar Talata.
Haruna ya ce: “Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta lura da wasu rahotanni da ke ɗora mata zargin baddala sakamakon yawan adadin ƙuri’un da ta loda kan Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe, wato IReV, a jihar Kogi. To ko ma daga ina, labarin ya fito dai ƙarya ce.
“Duk mai wata tababa ko shakku ya sani cewa sahihan adadin yawan waɗanda aka tantance karin shaidar zaɓen su na nan killace cikin Na’urar Tantance Adadin Masu Zaɓe (BVAS), wadda da ita ce ake amfani wajen tantance adadin masu rajistar da za su yi zaɓe a ranar zaɓen. Kuma adadin yawan masu zaɓen ha zai taɓa canjawa ba a cikin na’urar.”
Haruna ya ce batun duba adadin alƙaluman sakamakon zaɓe a manhaja ya danganta ne idan akwai ‘network’ ko babu.
Ya ce idan aka tura sakamakon zaɓe a IReV, to ba lallai ne ya isa a lokacin da aka tura ba. Kamar dai yadda saƙon tes na SMS ta waya ya ke, ba lallai ya isa lokacin da aka tura ba. Wani ya kan yi latti.
Haruna ya ce aikin Jami’an Zaɓe ne su danna ɗan maɓallin data kan Na’urar Tantance Masu Katin Zaɓe, wato BVAS domin tabbatar da an tura data a manhajar.
Sai dai kuma akwai zarge-zargen cewa a Jihar Imo an loda sakamakon zaɓe a IReV har da na yankunan da ba a ma yi zaɓen ba.
Discussion about this post