Jam’iyyar APC wadda Gwamna Hope Uzodinma ya sake tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin ta, ta lashe dukkan ƙananan hukumomin jihar 27, da yawan ƙuri’u 540,308.
PDP ta zo ta biyu da ƙuri’u 71,308, sai kuma LP wadda ta samu 64,081.
Hakan ya na nufin yanzu dai za a iya cewa ruwa ya ci kwarawan asali, Gwamnan Uzodinma ya lashe dukkan ƙananan hukumomi 27.
Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma, kuma ɗan takarar APC, shi ne ya lashe dukkan ƙananan hukumomin jihar 27.
A zaɓen gwamnan jihar wanda ya gudana a ranar Asabar, Uzodinma an bayyana cewa shi ne ya lashe mafi yawan ƙuri’un da aka tattara daga kowace ƙaramar hukuma, kamar yadda aka bayyana sakamakon zaɓen a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Owerri, babban birnin Jihar Imo.
Sai dai har yanzu INEC ta tafi hutu, zuwa lokacin tattara wannan labari, ba ta kai ga ambata sunan sa cewa shi ne ya yi nasara ba.
Uzodinma ya yi takara da masu adawa 17, waɗanda daga cikin su PDP da LP ce kaɗai su ka ɗan motsa, su ɗin ma ko an haɗa ƙuri’un su, Uzodinma ya yi masu fintinkau.
Discussion about this post