Ejan-ejan na jam’iyyar APC sun yi fatali da sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu, wanda INEC ta bayyana bayan komawa hutun awa ɗaya.
Sakamakon ya bayyana Gwamna Duoye Diri na PDP ya samu ƙuri’u 24,685, shi kuma ɗan takarar APC, Timipre Sylva, ya samu ƙuri’u 18,174.
Kafin bayyana sakamakon, APC ta yi tsammanin samun ƙuri’u masu yawa a ƙaramar ƙungiyar ta Ijaw ta Kudu, wadda kuma a can ne Mataimakin takarar Sylva ya fito, wato Maciver Joshua.
APC ta zargi INEC da yi mata surkulle, domin a cewar ejan ɗin, ƙuri’un da APC ta samu a can sun haura 70,000.
Yanzu dai ta tabbata cewa Gwamna Diri ya dire da ƙuri’u 175, ya bar Slyva na goge saleɓa da ƙuri’u 110,106.
Bayan INEC ta ci gaba da tattara Ƙaramar Hukumar Ijaw ta Kudu da ta yi saura, Gwamna Duoye Diri na Jihar Bayelsa ya kasance shi ne kan gaba kenan a sakamakon dukkan ƙananan hukumomi shida na jihar.
Diri ya samu ƙuri’u 175,196, shi kuma Timipre Sylva na APC ya samu 110,106.
Diri ya lashe dukkan ƙananan hukumomin jihar guda shida.
Abin da kawai ake jira a yanzu, shi ne INEC ta bayyana shi a matsayin gwamnan PDP da ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar.
Babu wata jam’iyya da ta samu ko da ƙuri’u 1,000 bayan PDP da APC a Bayelsa.
PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda INEC ta sake ɗage bayyana sakamakon zaɓe bayan ɓarkewar rincimi a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta sake ɗage bayyana sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa, bayan zuwa awa ɗaya, bayan ɓarkewar rincimi a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe da ke Yenagoa, babban birnin jihar.
Rincimin ya ɓarke lokacin da ejan-ejan su ka ƙi amincewa da sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Brass, wanda aka bayyana a cibiyar taskar ranar Litinin.
PREMIUM TIMES ta bada rahoton cewa ƙananan hukumomin Brass da Ijaw ta Kudu ne kaɗai su ka rage ba a bayyana sakamakon su ba a ranar Lahadi, har aka ɗage bayyana sakamakon zuwa wayewar garin yau Litinin.
Yayin da aka dawo tattara sakamakon zaɓe a yau Litinin, Baturen Zaɓe ya bayyana APC ta samu ƙuri’u 18,431, ita kuma PDP 12,602.
Sai dai kuma bayan sanarwar, ejan-ejan daga na APC da PDP ɗin duk sun ƙi yarda da sakamakon zaɓen, biyo bayan rahotannin ɓarkewar rikici a ƙaramar hukumar a lokacin zudanar da zaɓen a wasu mazaɓu.
Rincimi ya kai ga an ba hammata iska, har sai da jami’an tsaro suka shiga tsakani.
Daga nan INEC ta tsaida tattara sakamakon Ijaw ta Kudu.
Discussion about this post