Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa Ƙungiyoyin Ƙwadago na Ƙasa, wato NLC da TUC su tsunduma yajin aiki, domin bai kamata ba, kuma haramtacce ne.
Sanarwar da ta fito daga Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman a Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a ranar Litinin, ta ce tafiya yajin aikin kawai wata maƙarƙashiyar yi wa gwamnati zagon-ƙasa ce kawai.
Sanarwar Onanuga ta ce babu wani dalilin da zai sa ƙungiyar ƙwadago ta ƙaƙaba wa sama da mutum miliyan 200 wahala, saboda wani al’amari da ya shafi Shugaban NLC shi kaɗai.
Onanuga ya ce Gwamnatin Bola Tinubu ba ta goyon bayan jami’an tsaro su ci zarafin kowane ɗan Najeriya.
Ya ce to kuma bai kamata abin ya kai ga tafiya yajin aiki ba, tunda Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, ya kafa kwamitin bincike.
Daga nan ya ce Shugaban Ƙasa ya na kira da a janye batun tafiya yajin aiki, domin a sasanta cikin ruwan sanyi.
Sannan ya yi kiran da NLC da TUC cewa kada su tafi yajin aiki, su bi dokar kotu.
A na ta ɓangaren, ita ma Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU ta ce duk wani mamba ɗin ta ya fara yajin aiki daga yau Talata.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta umarci dukkan mambobin ta na faɗin ƙasar nan cewa su tsunduma yajin aiki daga yau Talata.
Sanarwar dai bin umarni ne ita ma ASUU ɗin ta yi daga Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, wadda ta bada umarnin cewa NLC da TUC su fara yajin aiki daga yau Talata.
Hakan dai ya biyo bayan dukan da ‘yan sandan Jihar Imo suka yi wa Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na Ƙasa, Ajaero ne farkon wannan wata a Owerri, babban birnin Jihar Imo.
Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke ne ya bada umarnin cewa ASUU ta bi umarnin NLC, ita ma ta tsunduma a yajin aikin.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙar da ya aika wa Shugabannin Shiyyoyi na ƙungiyar a ƙasar nan.
A ranar Litinin ce NLC ta bada sanarwar fara yajin aiki a ranar Talata, tun daga tsakar daren Litinin, 13 Ga Nuwamba.
Yajin aikin ya biyo bayan dukan da ‘yan sanda suka yi wa Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero a Owerri, ranar 1 Ga Nuwamba.
Kada a manta, a ranar Juma’a kotu ta haramta wa NLC da TUC tafiya yajin aiki, bayan Gwamnatin Najeriya ta hannun Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, ya shigar da ƙara.
Abin Da Ya Haifar Da Rikicin Tafiya Yajin Aiki:
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin NLC ta ce ‘yan sanda sun gwaggwabji shugaban ƙungiyar su na ƙasa, har suka kumbura masa kumatu.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta yi zargi tare da iƙirarin cewa ‘Yan Sandan Jihar Imo sun gwaggwabji Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero, ranar Laraba, a Owerri.
Tun da farko dai shugabannin NLC na ƙasa sun yi zargin cewa gungun ‘yan sanda waɗanda su ka yi shigar yaƙi sun kama Ajaero ranar Laraba ɗin a Owerri, babban birnin Jihar Imo.
“Sun kama shi a Sakateriyar NLC ta Jihar Imo, kuma har zuwa yanzu ba mu san inda suka tafi da shi ba,” haka babban jami’in yaɗa labarai na NLC ta ƙasa, Benson Upah ya bayyana.
Lamarin ya faru ne a ranar da aka shirya Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa za ta shirya zanga-zangar rashin amincewa da danne wa ma’aikatan Jihar Imo haƙƙi da ‘yancin su, wanda Gwamnatin Jihar Imo ke yi.
Sai dai kuma bayan sanarwar kama Ajaero, Rundunar ‘Yan Sandan Imo ta yi bayanin cewa ba kama shi ta yi ba.
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Imo, Henry Okoye ya fitar a ranar Laraba, ta ce sun ɗauke shi ne domin su “kare lafiyar sa”, dangane da harin wasu hasalallu su ka shirya kai masa, waɗanda ba su yarda a yi zanga-zangar ba.
Ajaero ya je Imo ne domin shirya zanga-zangar, wadda aka shirya za a yi a ranar Laraba ɗin.
‘Yan Sanda sun ce hayaniya ta ɓarke tsakanin ma’aikatan da ke goyon bayan yajin aikin da kuma waɗanda ba su goyon baya, har suka fara buga-in-buga a tsakanin su.
“Rincimi ya ɓaci, har hasalallu su ka fara naushi da kurufar Shugaban NLC, lamarin da ‘yan sanda suka gaggauta ficewa da shi Hedikwatar su ta Jihar Imo, domin kare lafiyar sa.”
Sanarwar ta ce daga nan sai Kwamishinan ‘Yan Sanda ya bada umarnin a gaggauta kai shugaban na NLC Asibitin ‘Yan Sanda na Owerri, domin a duba lafiyar sa.
‘Ƙarya ‘Yan Sanda Ke Yi, Su Suka Gwaggwabje Shi Ba Hasalallu Ba – NLC:
Cikin wata sanarwar ta daban a ranar Laraba ɗin sai, Kakakin Yaɗa Labaran NLC, Mista Upah, ya jajirce cewa ‘yan sanda kamun-kazar-kuku suka yi wa Shugaban NLC, ba kare lafiyar sa ba.
Ya tabbatar da cewa ‘yan sanda sun saki Ajaero, amma fa sun gwaggwabje shi, har sun sauya masa kamammu.
“Bayan sun kama shi, sun yi masa duka, kuma suka ɗaure masa idanu, suka arce da shi inda ba wanda ya sani. A can suka riƙa kwamtsar sa, har da kwalabe,” inji sanarwar.
Ya ce ba su samu sun yi magana da shi ba sai wajen 3:30 na yamma, a lokacin da ya ke asibitin ‘yan sanda.
Discussion about this post